An kama wani mutum da ake zargi da kashe wani jami’in Hukumar Kwastam ta Kasa lokacin da yake kan aiki, a kokarinsa na yin fasakwaurin wata mota kirar Toyata Corolla.
Ana dai zargin Abdulwasiu Salawudeen ne da kisan jami’in mai suna Aminu Abdullahi a Karamar Hukumar Yawuri ta Jihar ta Kebbi.
- Mataimakin Ciyaman ya rasu kwana 3 da rasuwar shugabansa
- Camfe-camfe da ke tattare da itaciyar kuka a Afirka
Babban Jami’in hukumar a Jihar, Ben Oramalugo,ne ya tabbatar da hakan a cikin wata sanarwa a ranar Litinin.
Ya ce an kama wanda ake zargin ne da sanyin safiyar Alhamis, 13 ga watan Yulin 2023, wajen misalin karfe 4:00 na yamma.
“An kama motar ce kirar Toyota Corolla 2015 mai lambar inji 2TBURHE3FC456204, wacce aka yi ittifakin wani mai fasakwauri ne ya tuka ta, inda ya take jami’inmu a kan titin Tarmac Road da ke Yawuri.
“An garzaya da jami’in zuwa Babban Asibitin gari Yawuri domin samun kulawar gaggawa, amma bayan ba shi taimakon farko, sai aka mayar da shi asibitin kashi da ke Wamakko a Jihar Sakkwato.
“Sai dai abin takaici, ya kwanta dama lokacin da ake kokarin kula da shi. Amma Alhamdulillah, mun sami nasarar kama wanda ake zargin mai suna Abdulwasiu Salawudeen, wanda ke tuka motar, kuma tuni mun kawo shi hekdwatar hukumarmu da ke Birnin Kebbi domin zurfafa bincike.