✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mataimakin Ciyaman ya rasu kwana 3 da rasuwar shugabansa

Mataimakin shugaban karamar hukumar ya rasu bayan gajeriyar rashin lafiya

Wani al’mari ya dabaibaye Karamar Hukumar Akure ta Arewa a Jihar Ondo, bayan rasuwar Mataimakin Shugaban Karamar Hukumar, Mista Anthony Adebusole.

Aminiya ta gano cewa Adebusola ya rasu kwanaki uku bayan rasuwar Shugaban Karamar Hukumar, Bankole Ogbesetore.

Da yake tabbatar da rasuwarsa a ranar Litinin, tsohon Kwamishinan Wasanni da ci Gaban Matasa, Saka Ogunleye, ya ce Mista Adebusola ya rasu ne bayan gajeriyar rashin lafiya a ranar Lahadi.

Mista Ogunleye, ya bayyana cewa rasuwar mataimakin shugaban karamar hukumar, rashi ne babba ga jama’a.

“Abin bakin ciki ne, kuma rashi babba da zan sanar da rasuwar mataimakin shugaban karamar hukumarmu, Honarabul Anthony Adebusola.

“Ya rasu ne a jiya [Lahadi] bayan gajeriyar rashin lafiya. Abin bakin ciki mun rasa zababbun shugabanninmu cikin mako guda,” in ji shi.

A makon da ya gabata ne, Mista Ogbesetore, tsohon shugaban karamar hukumar ya rasu bayan ya yi fama da wata cuta da ba a bayyana ba.

Marigayin, ya shafe sama da shekara guda a kwance yana jinya.

Lucky Aiyedatiwa, mukaddashin gwamnan jihar, ya kai ziyarar jaje gidan Mista Ogbesetore kafin rasuwar mataimakinsa.