Akalla mutum 200 ne aka yi wa fyade a watanni 10 na farkon shekarar 2020 a Jihar Kebbi.
Shugabar Zaki’s Gem Support Foundation, Nafisa Abubakar Zaki ce ta sanar da haka a taron kasa da kasa na 2020 kan cin zarafi na jinsi a Birnin kebbi.
- Buhari ya kori Shugaban Hukumar Samar da Ayyuka
- Uwa ta rataye ’ya’yanta 2 don ta yi lalata da kare
- Dan shekara 50 ya yi wa ’yar shekara 6 fyade a Kaduna
“An samu rahoto sama da 200 na fyade a Jihar Kebbi daga watan Janairu zuwa yau; kwanan nan kungiyarmu ta samu rahoto 45 na aikata laifukan fyade da muke kan aiki a kansu”, inji ta.
Nafisa ta koka cewa laifukan fyade sun zama ruwan dare a jihar kuma hakan na bukatar fadakar da mata, ’yan mata da iyaye kan yadda masu rauni za su kare kansu.
A cewarta, duk da cewa jihar ba ta da rumbun bayanan cin zarafi, amma ana hada kai da asibitoci, hukumar Hisbah ta jihar da sauran hukumomin tsaro domin samar da sahihan alkaluma.
Ta yaba wa gwamnatin jihar saboda kafa cibiyar kula da wadanda aka kai wa farmaki ta hanyar fyade da ke asibitin gwamnati a garin Kalgo.
A yanzu cibiyar za ta iya ba da kulawa ta fuskar zamantakewar dan Adam, shawara da kuma isar da taimako ga wadanda aka yi wa fyade.
Kungiyar ta ce gangamin na yaki da fyade da ke gudana a yanzu na daga cikin gangamin kwana 16 da Matan Majalisar Dinkin Duniya suka shirya don yaki da cin zarafi ta fuskar jinsi (GBV).