✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An yanke wa tsohon fira ministan Thailand daurin shekara 8

An yanke wa tsohon mai kungiyar kwallon kafa na Manchester City daurin shekara 8 kan caca, bashin banki da kuma rashawa

Kasar Thailand ta yanke wa tsohon fira ministanta kuma tsohon mai kungiyar kwallon kafa ta Manchester City, Thaksin Shinawatra hukuncin daurin shekara takwas.

Kotun Kolin kasar ta yanke wa Thaksin Shinawatra mai shekaru 74 hukuncin ne jim kadan da komawarsa kasar daga inta ya shekara 15 yana zaman mafakar siyasa.

An yanke tsohon mamallakin kungiyar kwallon kafa ta Manchester City  da ke Birtaniya hukuncin daurin ne kan laifukan cin bashin banki, caca da badakalar wani kamfani da aka same shi da su a lokacin da ya tsere daga kasar.

Thaksin Shinawatra ya dawo Thailand ne sa’o’i kadan kafin majalisar dokokin kasar ta nada dan jam’iyyarsa a matsayin sabon fira minista.

Bayan saukarsa a filin jirgin da misalin karfe 9 na safiyar Talata aka wuce da shi kotu, inda alkali ya yanke masa hukuncin zaman wakafin.A ranar Talata majalisar dokokin Thailand za ta nada attajiri Srettha Thavisin a matsayin sabon fira minista, inda zai jagoranci hadakar da jam’iyyarsa ta Pheu Thai za ta jagoranta.Ana ganin hadakar da sabon fira ministan zai jagoranta dai a matsayin dawowar tafiyar siyasar da Thaksin ke jagoranta a aksar.Kawo yanzu dai babu tabbacin ko a gidain yari zai yi zaman daurin da kotu ta yanke masa.