✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An yanke wa malamar jinya hukuncin daurin rai-da-rai kan kashe jarirai 7 a Birtaniya 

Alkalin da ya yanke hukuncin ya bayyana Lucy a matsayin 'mara tausayi'.

An yanke hukuncin daurin rai da rai ga wata ma’aikaciyar jinyar jarirai, Lucy Letby, wadda aka bayyana a matsayin macen da ta fi yi wa kananan yara kisan gilla a tarihin Birtaniya.

An yanke mata hukunci ne bayan samun ta da laifin kashe jariri bakwai da kuma yunkurin kashe karin wasu shida a wani asibitin yara da ke Countess of Chester.

Da gangan, Lucy Letby ta rika yi wa jarirai allura da sauran iska a cikin sirinji, kuma ta rika yi wa wasu dura da karfi, sannan ta bai wa jariri biyu guba da sinadarin insulin.

Bayan yanke mata hukunci, Lucy Letby ba ta nuna wata alamar nadama ba.

A halin da ake ciki dai Letby za ta shafe karashen rayuwarta a tsare, inda ta zama mace ta hudu a kasar da aka taba yankewa irin wannan hukunci, wanda shi ne mafi tsanani da ake yankewa mai laifi.

Alkalin kotun Mai shari’a Goss, ya bayyana laifin da Lucy ta aikata a matsayin abun kyama.

Ya ce “ta aikata abin da ya saba da tunanin dan Adam mai cikakken hankali, da ya san kimar lura da jarirai, kuma babban cin amanar wadanda suka yarda da aikin ma’aikatan lafiya ne.”

Alkalin ya bayyana ta a matsayin mara tausayi, wadda ke sanya damuwarta a cikin aikinta.

Lauyan da ke kare ta, Ben Myers KC, ya ce “tun bayan fara shari’ar Lucy ta ki musanta aikata laifin da ake zargin ta da aikatawa.

Ya ce dangane hakan ba shi da wani mataki da zai dauka da zai iya kai wa ga rage tsawon hukuncin da aka yanke mata.

Tun da fari dubban mutane a kasar sun shiga yin kiranye-kiranye don ganin an zartar mata da hukunci.

Bayan zartar da hukuncin mutane sun nuna farin cikinsu tare da fatan hakan zai zama izina ga masu hali irin nata.