Kasar Thailand ta yanke wa tsohon fira ministanta kuma tsohon mai kungiyar kwallon kafa ta Manchester City, Thaksin Shinawatra hukuncin daurin shekara takwas.
Kotun Kolin kasar ta yanke wa Thaksin Shinawatra mai shekaru 74 hukuncin ne jim kadan da komawarsa kasar daga inta ya shekara 15 yana zaman mafakar siyasa.
- NAJERIYA A YAU: Yadda Wike Ya Kaɗa Hantar ’Yan Abuja
- An yanke wa malamar jinya hukuncin daurin rai-da-rai kan kashe jarirai 7 a Birtaniya
An yanke tsohon mamallakin kungiyar kwallon kafa ta Manchester City da ke Birtaniya hukuncin daurin ne kan laifukan cin bashin banki, caca da badakalar wani kamfani da aka same shi da su a lokacin da ya tsere daga kasar.
Thaksin Shinawatra ya dawo Thailand ne sa’o’i kadan kafin majalisar dokokin kasar ta nada dan jam’iyyarsa a matsayin sabon fira minista.