Shugaban Karamar Hukumar Akwanga da aka sace a Jihar Nasarawa, Safiyanu Isah Andaha, tare da wasu mutum uku sun kubuta bayan an biya kudin fansa miliyan 10.
Aminiya ta ruwaito yadda aka sace shugaban tare da abokinsa, Adamu Custom da wasu mutum biyu, a kan titin Akwanga zuwa Andaha a daren Litinin.
Wani makusancin shugaban karamar hukumar, wanda ya bukaci a sakaya sunansa, ya shaida wa Aminiya cewa an sako duk wadanda abin ya shafa ne bayan an biya kudin fansa.
Majiyar ta ce “An sake su ne a daren Talata da misalin karfe 9 a bayan wani gidan mai da ke kan titin Bayan Dutse, kuma an biya kudin fansa Naira miliyan 10.”
Majiyar ta ce shugaban Karamar Hukumar ya bayyana cewa maharan suka ci zarafinsu lokacin da suka sace su.
Aminiya ta samu labarin cewa jim kadan bayan sakin su aka garzaya da su zuwa Cibiyar Kiwon Lafiya ta Tarayya (FMC), da ke Keffi don duba lafiyarsu.