✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An sake rufe Asibitocin bogi 6 a Oyo

An ɗauki matakin rufe Asibitocin ne domin tabbatar da manufar gwamnati ta kare lafiyar al’umma.

Gwamnati ta sake bayar da umarnin rufe wasu Asibitoci masu zaman kansu guda 6 da suke gudanar da ayyukan kula da lafiyar jama’a ta haramtacciyar hanya a Jihar Oyo.

Umarnin rufe Asibitocin na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Ma’aikatar Lafiyar jihar ta aika wa kafofin labarai a ranar Alhamis.

Da yake yi wa manema labarai karin haske a Ibadan, babban birnin jihar, Shugaban Hukumar Yaƙi da Asibitocin Bogi, Dokta Adekunle Aremu, ya ce an gano cewa Asibitocin shida da aka rufe suna horas da mutanen da ba su da ilimi da kwarewa a kan aikin kiwon lafiya kuma suke gudanar da ayyuka a matsayin likitoci da ma’aikatan jinya.

Ya ce an ɗauki matakin rufe Asibitocin ne domin tabbatar da manufar gwamnati ta kare lafiyar al’umma a jihar.

Dokta Aremu ya ƙara da cewa za a hukunta dukkan waɗanda aka samu da karya dokar kiwon lafiya a jihar.

Ya roƙi jama’a da su taimaka wajen bayar da gudunmawar tona asirin irin waɗannan Asibitocin bogi ta hanyar miƙa rahoto ga mahukunta.

Ya shawarci jama’a da su yi wa kansu karatun-ta-nutsu ta fannin yin amfani da halastattun Asibitoci da ɗakunan shan magani da suke da ƙwararrun ma’aikata domin kare kansu daga faɗawa hannun bara-gurbin ma’aikata.

Wakilinmu ya ruwaito cewa Asibitocin da aka rufe sun haɗa da New Jobi Memorial Hospital da Omolara Clinic and Maternity Home da Amazing Grace Medical Clinic da Emiloju Clinic and Maternity Center da Safeway Clinic da Emilagba Clinic and Maternity Center.

Aminiya ta ruwaito cewa a kwanan baya ma ma’aikatar lafiyar jihar ta bayar da irin wannan umarni ga wasu Asibitoci masu zaman kansu da aka kama likitocin bogi suna ikin tiyata ba tare da ƙwarewa ba.