✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za mu duba yiwuwar kafa ’yan sandan jihohi — Tinubu

Ba abu ba ne da kawai za a fada cikinsa kai tsaye, yana bukatar nazari sosai.

Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da a soma nazari kan batun kafa rundunar ’yan sandan jihohi a kasar.

Ministan Labarai da wayar kan al’umma, Mohammed Idris ne ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai a Fadar Gwamnatin Tarayya da ke Abuja.

Wannan dai a cewar ministan na daga cikin batutuwan da aka tattauna a wajen wani taron gaggawa da Tinubun ya jagoranta da gwamnonin jihohin kasar 36 ranar Alhamis a fadarsa.

Taron dai ya mayar da hankali ne kan nazarin muhimman matsalolin da ke addabar kasar yanzu da zimman nemo bakin zaren warware su.

Batutuwan dai sun hada da na tsaro, da tsadar rayuwa da karancin abinci da makamantansu kamar yadda ministan ya sanar da manema labarai bayan tashi daga zaman.

Ya ce zaman ya kunshi shawarwari kan yadda za a hada kai tsakanin jihohi da gwamnatin tarayya domin magance matsalolin da ke ci wa kasar tuwo a kwarya.

Ya kuma ce taron ya mayar da hankali kan yadda za a dakile matsalar ɓoye amfanin gona da sauyan hatsi da wasu manoma da ’yan kasuwa ke yi.

“Ba ma son rabe-rabe tsakanin jihohi da Gwamnatin tarayya, ko da a wace jam’iyya kake, an yi shawawari kan yadda za a ciyar da kasar gaba”, in ji shi.

Dangane da ’yan sandan jihohi, ministan ya ce Shugaba Tinubu ya amince cewa a duba maganar yiwuwar kafa ’yan sandan a fadin jihohin kasar, maimakon dogara kacokam kan ’yan sandan Gwamnatin Tarayya.

“To sai dai wani abu ne da yake bukatar nutsuwa a duba a kuma tantance, ba abu ba ne da kawai za a fada cikinsa kai tsaye, yana bukatar nazari sosai”, in ji ministan.

Ministan ya kara da cewa taron ya amince da shugabannin hukumomin tsaron kasar su yi aiki tare da gwamnonin jihohi wajen sa kafar wando ɗaya da wadanda suka boye kayan abinci da muhimman kayan masarufi domin su yi tsada sannan su sayar da su.

Kazalika, shugaban kasar da gwamnonin sun kuma amince cewa kasar ba ta bukatar shigo da kayan abinci daga waje, domin sauko da farashinsa, suna masu cewa kasar na iya dogara da abincin da al’ummarta ke nomawa.

Daga cikin wadanda Aminiya ta hango a taron akwai Mataimakin Shugaban Kasa Kashim Shettima; Sakataren Gwamnatin Tarayya, George Akume; Sufeto-Janar na ‘yan sanda, Kayode Egbetokun; Mai Bai wa Shugaban Kasa Shawara kan Harkokin Tsaro, Nuhu Ribadu da Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, Femi Gbajabiamila.

Gwamnonin da suka halarci taron sun hada da; Abdulrahman Abdulrazaq; (Kwara) da Hope Uzodinma; (Imo); Farfesa Babagana Zulum (Borno); Godwin Obaseki (Edo) Sim Fubara (Ribas) Biodun Oyebanji (Ekiti) Charles Soludo (Anambra), Caleb Mutfwang (Filato) da Uba Sani (Kaduna) da sauransu.

A Larabar da ta gabata ce Majalisar Sarakunan Arewa ta yi koke dangane da matsi da kuncin rayuwa da al’ummar kasar ke fuskanta a dalilin tsadar kayan abinci baya ga matsalar tsaro.

Gwamnatin Tarayyar dai ta sha nanata cewa sauye-sauyen tattalin arziki da Tinubu ya yi ciki har da cire tallafin man fetur ya zama dole, inda ta kara da cewa wadannan matakan za su haifar da riba nan ba da jimawa ba.