✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan Najeriya na cikin ƙunci a Gwamnatin Tinubu — Kukah

Kukah yana roƙon 'yan Najeriya da su jajirce saboda gina al'umma ta gari yana ɗaukar lokaci.

Bishop ɗin ɗarikar Katolika, Bishop Matthew Hassan Kukah ya ce ‘yan Najeriya na cikin ƙunci, yana mai kira ga shugaban ƙasa Bola Tinubu da ya gaggauta buɗe duk wasu kafofi da jama’a da za su fara cin moriyar manufofinsa.

Bishop Kukah ya ce duk da cewa “ƙuncin da ’yan Nijeriya ke fuskanta ba da gayya ba ne”, amma dai ’yan ƙasar na cikin raɗaɗi sanadiyyar manufofin da gwamnatin ta kawo da fatan cewa za su amfani ba tare da ɗaukar wani dogon lokaci ba.

Kalaman babban limamin na zuwa ne a wannan Larabar yayin wata hirarsa da manema labarai bayan ganawa da Shugaba Bola Ahmed a Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja.

Bishop ɗin ya ce duk da cewa a yanzu ana cikin wani lokaci mai cike da ƙalubale, ya roƙi ’yan Najeriya da su ƙara jajircewa saboda “gina al’umma ta gari da assasa tubalin ci gaban kasa yana ɗaukar lokaci mai yawa.

“Na zo ganin Shugaban ƙasa tare da Daraktan Cibiyar Kukah.

“Mun zo ne don tattaunawa da shugaban ƙasa da sabunta gayyatar da muka yi masa a baya,  domin taron da za mu so ya halarta mai taken haɗin kan ƙasa.

“Saboda haka, wannan shi ne ainihin abin da muka zo don tattaunawa ke nan.”

Da aka tambaye shi ya kan ma’unin ƙwazon gwamnatin Tinubu a tsawon shekara ɗaya, ya ce “Na tabbata mutane da yawa za su gaya maka cewa shekara ɗaya ba ta isa a yanke hukunci ba.

“Amma duk da haka, a wannan yanayi da halin da ake ciki, mun san cewa dukanmu muna cikin mawuyacin hali.

“Yan Najeriya na fama da ƙuncin rayuwa daban-daban kuma suna fuskantar ƙuncin da ba a jefa su ciki da gayya ba.

“Amma sakamakon wasu shawarwari ne na manufofin da ake fatan zuwa wani lokaci  jama’a za su ji daɗin gyaran.