Ƙungiyar Matan Gwamnonin Arewa ta koka kan yadda ake samun ƙaruwar ɗabi’ar shaye-shayen miyagun ƙwayoyi da sauran kayan maye a tsakanin matan aure a gidajensu na aure.
Shugabar Ƙungiyar, Uwargidan Gwamnan Jihar Gombe, Hajiya Asma’u Muhammad Inuwa Yahaya, ta ce ƙungiyarsu ta kaɗu matuƙa kan yadda lamarin shaye-shayen ya yi ƙamari ya wuce kan ‘yan mata ya shiga gidan matan aure.
- Ƙungiyar Ƙwadago ta yi watsi da N48,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi
- An gurfanar da Emefiele kan kashe N18.96bn wajen buga takardun kuɗi na N684.5m
Asma’u , ta ce cikin ajandar taron nasu ne suka ga dacewar tallafa wa Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi (NDLEA) na ganin yadda za a gyara tarbiyar waɗanda suka kangare a dalilin shaye-shaye.
Ta ce, bayan nan sun shirya tallafa wa mata da kayan koyon sana’o’i irin injinan markaɗe da keken ɗinki da sauransu.
“Yanzu akwai mata masu sayan kayan shaye-shaye da za su kira ta waya a kawo musu har gida wanda hakan ba ƙaramin bala’i ba ne a tsakanin al’umma,” inji ta.
Shugabar Ƙungiyar, ta ƙara da cewa ƙungiyarsu ta zaɓi Gombe ne domin wannan taro sannan su ba da tallafin ga mata don ganin an rage musu raɗaɗin rayuwa su samu hanyar dogaro da kansu.
Kazalika, ta yi kira ga sarakunan gargajiya da shugabanin addinai da cewa sai sun shigo ciki sun taimaka domin shawo kan wannan lamari.