Babban Basaraken Jihar Oyo, Mai Martaba Olubadan na Ibadan, Oba Mohood Lekan Balogun, Alli Okunmade na biyu ya rasu.
Sarkin ya rasu ne bayan shekaru biyu da hawa gadon sarautar.
Oba Balogun ya rasu ne a Asibitin koyarwa na Jami’ar (UCH) da ke birnin Ibadan a ranar Alhamis din da ta gabata.
Gwamnan Jihar Oyo, Seyi Makinde ne da kansa ya bayyana rasuwar sarkin a cikin wata sanarwa da ya fitar a daren ranar Alhamis.
- Kotu ta raba auren shekara 14 saboda rashin kulawa
- ’Yan Najeriya sun fi wata 6 suna azumi kafin Ramadan — Alaramma Mujahid
Gwamnan ya bayyana Oba Balogun a matsayin wani gwarzo abin koyi, wanda ya kawo ci gaba da ɗaukakar masarautar, kuma babban abin alfahari.
Ya bayyana marigayin a matsayin wanda ya yi fice a ƙasar Ibadan cikin ‘yan shekaru biyu na mulkinsa.
Gwamnan ya miƙa ta’aziyyarsa ga Masarautar Ibadan da Majalisar Sarakunan Gargajiya ta Jihar Oyo da kafatanin al’ummar Ibadan da Jihar Oyo baki ɗaya.
Gwamnan ya ce “Babban bango ya fadi; Oba Dokta Balogun ya riga mu gidan gaskiya.
“A madadin gwamnatin Jihar Oyo, ina jajanta wa iyalan Oba Dokta. Balogun, masarautar Ibadan, da kuma daukacin majalisar sarakunan gargajiya ta jihar Oyo da kuma mutanen Ibadan. Addu’ata ce Allah ya jikan marigayi Sarkinmu.”
Gwamnan ya bayyana Sarkin a matsayin haziki, jajirtacce kuma gogagge a fanninsa na sarautar gargajiya.
Wakilinmu da ke Ibadan ya ruwaito daga wata majiyar zuriyar marigayi Oba Lekan cewa ana sa ran yi masa jana’iza kamar yadda Addinin Musulunci ya tanadar a yau Juma’a da misalin ƙarfe 4 na Yamma.
Majiyar ta ce za a binne gawar marigayin ne a Fadar Aliwo da ke Ibadan, inda aka binne Sarakunan da suka gabata da suka fito daga zuriya ɗaya.
Ana iya tuna cewa, Gwamna Seyi Makinde ne ya tabbatar da naɗin Oba Lekan Balogun a matsayin Olubadan na 42 a wajen wani gagarumin bikin miƙa sanda da aka gudanar a ranar 11 ga watan Maris na 2022 a birnin Ibadan.