✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tsohon Gwamnan Oyo Olunloyo ya riga mu gidan gaskiya

Ya rasu saura kwanaki 9 kacal ya cika shekaru 90 a doron ƙasa.

Tsohon Gwamna Jihar Oyo, Omololu Olunloyo ya riga mu gidan gaskiya.

Wata sanarwa da iyalansa suka fitar ta ce ya rasu yayin da rage kwanaki tara kacal ya cika shekaru 90 a doron ƙasa.

Tsohon gwamnan wanda aka haifa a ranar 14 ga watan Afrilun 1935, ya rasu ne da misalin ƙarfe 1:40 na daren ranar 6 ga watan Afrilun 2025.

Bayanai sun ce a bayan nan ya yi ’yar taƙaitacciyar jinya da ke da alaƙa da mutanen da shekarunsu suka ja.

Olunloyo ya riƙe muƙamin Gwamnan Oyo daga ranar 1 ga watan Oktoban 1983 zuwa 31 ga watan Disamban 1983 lokacin da Janar Muhammadu Buhari ya karɓi mulki.