✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

APC ta kori tsohon Gwamnan Osun, Aregbesola daga jam’iyyar

Wannan dai ya nuna yadda rikicin cikin gida ke ƙara ƙamari a APC a Jihar Osun.

Jam’iyyar APC a Jihar Osun, ta kori Tsohon Gwamnan Jihar kuma Tsohon Ministan Cikin Gida, Rauf Aregbesola, bisa zargin cin amanar jam’iyyar.

Wannan ya biyo bayan ƙorafe-ƙorafen da shugabannin jam’iyyar na Ƙaramar Hukumar Ilesa ta Gabas suka gabatar.

Sun nemi a ɗauki mataki a kan Aregbesola saboda zargin kafa ƙungiyoyin da ke raba kan jam’iyyar da yin haɗin gwiwa da jam’iyyun adawa don raunana APC a Osun.

A cikin wata wasiƙa da kwamitin zartarwa na APC na Osun ya aike wa shugaban jam’iyyar na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, sun bayyana cewa Aregbesola ya kafa wata ƙungiya mai suna “Omoluabi Caucus” ba tare da amincewar jam’iyyar ba.

Sannan ya yi furuci na ɓatanci ga shugabannin jam’iyyar, ciki har da Shugaba Bola Tinubu, tsohon gwamna Bisi Akande, da kuma tsohon gwamna Gboyega Oyetola.

Kwamitin ladabtarwa na jam’iyyar ya rubuta wa Aregbesola wasiƙa, inda suka ba shi sa’o’i 48 ya mayar da martani kan zarge-zargen da ake masa.

Sai dai Aregbesola bai yi wani jawabi ba kan hakan ba, wanda ya sa jam’iyyar ta ɗauki matakin korarsa.

Wannan rikici ya ƙara nuna yadda rikicin cikin gida ke ƙara tsamari a jam’iyyar APC a Jihar Osun, musamman dangane da bambance-bambancen da ke tsakanin Aregbesola da wasu shugabannin jam’iyyar a matakin jiha da na ƙasa.