✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tinubu ya gana da Fubara a Legas

Idan ba a manta ba Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci a Jihar Ribas, tare da dakatar da Gwamna Fubara.

Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya gana da gwamnan Jihar Ribas da aka dakatar, Siminalayi Fubara, a gidansa da ke Legas.

Wannan ganawar na cikin ƙoƙarin warware rikicin siyasa da ya addabi jihar.

Fubara, ya samu saɓani da ubangidansa na siyasa, Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, bayan hauwansa mulki.

Saɓani kan ikon mallakar kuɗin jihar da naɗin muƙamai ya janyo rarrabuwar kawuna a cikin gwamnatin jihar da kuma majalisar dokokin jihar.

A watan Maris 2025, Shugaba Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci a jihar Ribas tare da dakatar da Gwamna Fubara, mataimakiyarsa, da kuma ‘yan majalisar dokokin jihar baki ɗaya.

Ya naɗa tsohon Hafsan Soja, Vice Admiral Ibokette Ibas (mai ritaya), a matsayin kantoma da zai kula da harkokin jihar.

“Tun da rikicin ya ci gaba da faruwa, babu yadda za a yi gwamnati mai bin doka da ƙa’ida ta ci gaba,” in ji Shugaba Tinubu a wani jawabi da ya yi.

“Komai ya ta tsaya cak a jihar tun da aka fara rikicin.”

“Gwamnan… ya rushe majalisar dokoki tun ranar 13 ga wata. Disamban 2023, kuma har yanzu bai gyara ta ba,” in ji Tinubu.

“Duk ƙoƙarina na yin sulhu babu abin da ya sauya.”

Duk da cewa ba a bayyana cikakken bayani kan ganawar da suka yi ba, an ce hakan na cikin ƙoƙarin samar da zaman lafiya tsakanin ɓangarorin biyu.

Wannan ganawar ta biyo bayan wata ganawa da suka yi a Landan watanni da suka gabata.

Majalisar Tarayya ta goyi bayan matakin Tinubu, kuma ta buƙaci a kawo ƙarshen dokar ta-ɓaci cikin watanni shida tare da kafa kwamitin sulhu domin warware matsalar.