Sarkin Yarbawan Jihar Kano, Oba Murtala Alimi Otisese ya shawarci masu faɗa- a-ji a ƙasa su duba yiwuwar dawo da salon mulkin al’umma irin na sarakuna da aka fara yi a 1914 bayan Turawan mulkin mallaka sun haɗe Nijeriya.
Ya ce, irin wannan salon mulki na kishin ƙasa da adalci ne marigayi Mai martaba Olubadan na Ibadan Oba Lekan Balogun ya fara yi a shekara biyu a karagar mulki kafin Allah Ya karɓi ransa.
Ya kawo shawarar ce a hirarsa da Aminiya jim kaɗan bayan kammala addu’ar kwana bakwai da rasuwar Sarkin na Ibadan.
- Gwamnatin Tarayya ta yi wa maniyyata tallafin kuɗin Hajjin bana
- ’Yan sanda sun miƙa wa sojoji Sarkin da ake nema ruwa a jallo kan kisan dakaru a Delta
Babban Limamin Ibadan Sheikh Abdulganiyu Abubakar Agbotomokekere ne ya jagoranci limamai da malamai wajen gudanar da addu’ar da aka yi a Zauren Taro na Mapo da ke tsakiyar birnin Ibadan Hedikwatar Jihar Oyo.
Oba Muritala Alimi Otisese wanda ya jagoranci wasu sarakunan Yarbawan Arewa zuwa wajen addu’ar, ya ce, marigayi Olubadan na Ibadan cikin shekara biyu da ya yi a kan karaga ya yi amfani da ilimi da hikima da basira wajen yin koyi da sarakunan baya, lamarin da ya kai shi ga samun nasarar haɗa kan al’umma musamman ’yan siyasa da aka dogara da su wajen samun kyakkyawan jagoranci.
“Kuma dukkanmu ’yan asalin Ibadan da al’ummar Jihar Oyo da ƙasa baki ɗaya mun isa shaida kan salon mulkin adalci ba tare da son zuciya ko kwaɗayin abin duniya da marigayi Oba Lekan Balogun ya jajirce wajen aiwatarwa a ƙanƙanin lokaci a kan karaga.
“Tarihi ba zai taɓa mantawa da marigayi Olubadan ba a kan ci gaban da aka samu a Masarautar Ibadan wajen tabbatar da tsaro da janyo baƙi na ciki da wajen Nijeriya da kyautata zamantakewa a tsakanin baƙi da ’yan gari tare da kyawawan shawarwari da yake b ’yan siyasa da a kowane lokaci.
Marigayi Olubadan kan tunatar da jama’arsa kan alfanun yin siyasa ba da gaba ba domin samun zama lafiya da ci gaban masarautar da Jihar Oyo baki ɗaya,” in ji shi.
Oba Murtala Alimi Otisese wanda ɗan asalin Ibadan ne ya ce, a madadin sarakunan Yarbawan Arewa Arewa yana yin kira ga sarakuna da shugabanni su yi koyi da marigayi Olubadan na Ibadan ta fannin yin adalci ba tare da nuna bambancin addini ko ƙabila da ɓangaranci ba domin ci gaban Nijeriya.
“Kuma ya kamata mu yawaita roƙon Allah Ya tsame ƙasar mu daga ƙuncin rayuwa da taɓarɓarewar tsaro,” in ji shi.
Bayan kammala addu’o’in, sarakunan Yarbawan Arewa sun ziyarci gidan marigayi Olubadan domin miƙa saƙon ta’aziyyar ɗaukacin Yarbawan Arewa ga iyalansa.
Ɗan uwan marigayin Sanata Kola Balogun ne ya yi masu maraba a madadin zuriyar gidan.
Otun Olubadan kuma tsohon Gwamnan Jihar Oyo, Sanata Rashid Ladoja da Sarkin Musulmin Ƙasar Yarbawa, Alhaji Dauda Akinola da Shugaban Ƙungiyar ’Yan Asalin Ibadan (CCII), Cif Niyi Ajewole da Iyaloja (Uwar ’Yan Kasuwan) Jihar Oyo, Hajiya Saratu Konibaje suna daga cikin manyan mutanen da suka halarci wajen addu’ar.
An rufe manyan kasuwannin Ibadan a ranar domin girmama marigayi Sarkin Ibadan Oba Lekan Balogun.