Gwamna Seyi Makinde na Jihar Oyo ya bayar da umarnin rufe dukkan kasuwanni da shaguna da hana zirga-zirgar ababen hawa daga ƙarfe 6 na safiyar yau Asabar zuwa 6 na yamma saboda zaɓen ƙananan hukumomi da za a gudanar a faɗin jihar.
Sakataren Gwamnatin Jihar, Farfesa Olanike Adeyemo ne ya fadi haka a ranar Juma’a cikin wata sanarwa da aka aika wa kafofin labarai a Ibadan, babban birnin Jihar ta Oyo.
- Ƙarancin man fetur ya ƙara ta’azzara a Sakkwato
- Dalilin janye wa hukumar yaƙi da rashawa ta Kano jami’an tsaro — ’Yan sanda
Da yake yi wa ’yan jarida bayani a ranar Juma’a kan irin matakan tsaro da suka ɗauka, Kwamishinan ’yan sandan jihar, CP Adebola Hamzat, ya ce an girke jami’an tsaro dubu 12 a sassa daban-daban domin tabbatar da gudanar da zaben na yau Asabar lami lafiya.
Kwamishinan ’yan sandan ya shawarci ’yan kasuwa da jama’ar gari da su tabbatar da sun girmama doka da oda musamman wajen bin umarnin gwamnati da ta hana zirga-zirgar ababen hawa da rufe kasuwanni da shaguna daga ƙarfe 6 na safe zuwa 6 na Yammacin wannan rana.
Shi kuwa Shugaban Hukumar Zaben Oyo (OYSIEC), Are Isiaka Abiola Olagunju (SAN), ya nemi jami’an tsaron da su yi duk mai yiwuwa wajen kama mutanen da suka kai wa jami’an hukumar hari a garin Okeho a ƙarshen makon jiya.
Ya ce duk da yake maharan ba su yi nasarar kwace wasu kayan aiki ko jikkata jami’an hukumar ba, akwai buƙatar bankaɗo waɗannan mutanen domin gano nufin su da magance aukuwar irin haka a nan gaba.
Bayanan da Aminiya ta tattaro sun nuna cewa jam’iyyun siyasa 18 da aka yi wa rajista sun tsayar da ’yan takara dubu 4 da 900 da ke neman kujerar Shugabanni da Kansiloli a Kananan Hukumomi 33 na jihar.
Alkalumma da Hukumar Zaben ta fitar sun nuna cewa jama’a za su kaɗa kuri’un ne a rumfunan zabe 4783 da ke faɗin jihar.
A wani bincike, Aminiya ta gano cewa tun kafin isowar wannan rana jam’iyyar PDP mai mulki a jihar ta yi yunƙurin yi wa masu zaɓe kamun-kafa, inda ta tura ’yan takara zuwa mazabu domin yi musu shela da raba kayan abinci da na masarufi ga magoya bayanta.
Sai dai su ma sauran jam’iyyun musamman jam’iyyar APC ta ɗauki irin wannan salo na shela.
A yayin da jam’iyyun PDP da APC suka tsayar da ’yan takara a dukkan mazabu, sauran jam’iyyun adawa ba su iya yin hakan ba.