✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An sace iyalan Jami’in Kwastom a Abuja

Wasu ’yan ta’adda sun sace matar wani jami’in hukumar kwastom da ‘ya’yansa uku da wani kaninsa a gidansu da ke unguwar Shagari Kwatas da ke…

Wasu ’yan ta’adda sun sace matar wani jami’in hukumar kwastom da ‘ya’yansa uku da wani kaninsa a gidansu da ke unguwar Shagari Kwatas da ke Dei-dei da ke Abuja.

Wani dan banga ya shaida wa wakilinmu cewa ’yan bindigar sun shiga unguwar ne kai tsaye suka shiga gidan ma’aikacin suka yi awon gaba da iyalansa da sanyin safiyar ranar lahadi.

ya ce, ““Sun kwashe sama da sa’o’i biyu kafin su fita daga unguwar Dei-dei suka wuce Dakwa da ke makwabtaka da su.

“Mai gidan a da yana aiki a Abuja ne, a lokacin da yake nan, kullum akwai  ’yan sandan Rapid Response Squad (RRS)a tare da shi. Amma yanzu ba su nan tun da ya koma Legas aiki, amma  iyalansa na zaune a gidan.”

Wani rahoto da muka samu na tabbatar da cewa ’yan ta’addar sun saki matar jami’in Kwastam din da ke da tsohon ciki, amma sun tafi da ’ya’yanta da kuma kanin mai gidan.

Dokta Alhassan Musa Babachukuri, Dagacin Dakwa, ya ce, ’yan bindigar sun so su kara dibar wasu mutanen a yankinsa, amma suka tsere bayan barin wuta da jami’an tsaro suka yi musu a garin.

Babachukuri ya ce, ’yan bindigar sun yi sansani a gefen Dutsen Zuma, daf da kauyen Chachi.

Ya yi kira ga hukumomi su yi gaggawar daukar mataki akan ’yan ta’addar tun kafin su ci karfin yankin su gagari kowa.

Duk kokarin da wakilinmu ya yi domin jin ta bakin mai magana da yawun rundunar ’yan sandan Abuja, SP Josephine Adeh, domin jina ina aka kwana, ya ci tura.