Sojojin Najeriya sun kai wani mummunan harin ramuwar gayya kan sansanonin ’yan ta’adda a Dajin Sambisa, inda suka kashe mayaƙa da dama tare da tarwatsa maɓoyar miyagun.
Sojoji sun ƙaddamar da wannan farmaki ne bayan kisan abokan aikinsu huɗu da ’yan ta’adda suka yi a farkon wannan makon.
Kai tsaye sojojin suka kai hari kan sansanonin ’yan ta’addar da ke Garin Malam Ali da Garin Glucose da kuma da Ukuba, waɗanda ke cikin Dajin Sambisa.
Wannan matakin da aka ɗauka ya biyo bayan jerin hare-hare da ake zargin mayaƙan Boko Haram ne suka kai a ranar Talata kan sansanonin sojoji guda uku a Rann da Gajiram da kuma da Dikwa a Jihar Borno, wanda ya yi sanadiyar mutuwar sojoji hudu.
- NAJERIYA A YAU: Shin Jam’iyyar NNPP Za Ta Kai Labari A 2027?
- An kama wata mata kan safarar makamai zuwa Katsina
Duk da cewa sojojin sun yi nasarar murƙushe wadancan hare-haren na farko, tare da yi wa ’yan tayar da ƙayar bayan ɓarna a Dikwa da Gajiram, aikin ramuwar gayya da ya biyo baya na nufin gurgunta ƙarfin ’yan ta’addar.
Majiyoyin soji, waɗanda suka nemi a sakaya sunansu saboda muhimmancin lamarin, sun bayyana cewa haɗin gwiwar da aka yi da mayaƙan Civilian CJTF ya ɗauki sama da sa’o’i shida, daga misalin karfe 6 na safe a ranar Laraba har zuwa tsakar rana a ranar Alhamis.
Wani hafsan soja ya bayyana cewa, “Aikin ba mai sauƙi ba ne, amma duk mun yi farin ciki da nasarar da aka samu,” yana mai jaddada ƙudurinsu na ci gaba da yaƙi.
Ya ci gaba da cewa, “Ana ci gaba da aikin, muna cikin shirin yaƙi, kuma ya kamata mu yi nasara wannan yakin.”
Jami’in ya kuma tabbatar da cewa wasu ’yan ta’addar sun gudu da raunukan harbin bindiga, inda suka bar makamai da kayan aiki, ciki har da kayan hada abubuwan fashewa, yayin da aka “kashe” da dama daga cikinsu.
Babban Jami’in Yada Labarai na Sojoji a Hedikwatar Rundunar Sojoji ta Kasashe (MNJTF) a N’djamena, Chadi, Laftanar Kanar Olaniyi Osoba, ya tabbatar da wannan aikin, da cewa, “Dakarun Operation Hadin Kai na Arewa maso Gabas da Civilian JTF sun tarwatsa maɓoyar ’yan ta’adda a Dajin Sambisa a ranar 15 ga Mayu, 2025.”
Ya ƙara da cewa, “’Yan ta’addar sun tsere, inda suka bar makamai, alburusai, da kayan haɗa bama-bamai. Wannan aikin wani ɓangare ne na ƙoƙarin da ake yi na ƙwace Dajin Sambisa da kuma daƙile ayyukan ’yan ta’adda.”
Nasarar wannan aikin ta nuna ƙudirin rundunar sojin Najeriya na ci gaba da bin diddigi tare da raunana ƙarfin ’yan ta’adda a yankin Arewa maso Gabas bayan hare-hare kan dakarunta.