✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shugaban kasar Iran ya rasu a hatsarin jirgin sama

Shugaba Iran Ebrahim Raisi tare da Ministan Harkokin Waje Hossein Amirabdollahian sun mutu sakamakon hatsarin helikwafta a kan iyakar kasarsu da Azrabijan

Shugaban Kasar Iran Ebrahim Raisi tare da Ministan Harkokin Wajen ƙasar Hossein Amirabdollahian sun mutu sakamakon hatsarin helikwafta da ya rutsa da su a ranar Lahadi.

Wani wani jami’in gwamnatin ƙasar ne ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters hakan.

Wani jirgi mai saukar ungulu dauke da shugaban kasar Iran Ebrahim Raisi da ministan ya yi hatsari a arewa maso yammacin kasar, da yammacin ranar Lahadi.

Bayan faruwar lamarin, kafofin yada labaran Iran sun ce an dukufa lalube da aikin ceto a wurin da jirgin ya faɗa amma rashin kyan yanayi ya hana su ganin sa.

Tashar talabijin ta Aljazeera ta ce Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatollah Ali Khamenei ya bayyana damuwarsa kan lamarin a wata ganawa wasu jagororin kasar.

Ya yi kira ga ’yan kasar su rungumi kaddara, a lokacin yana mai fatan Allah a dawo musu da shugaban nasu cikin aminci.

Ya kuma ce da yardar Allah ba za a samu tangarda a harkokin gudanar da mulkin kasar ba.

Shugaban ya gamu da wannan tsautsayi ne akan hanyarsa ta dawowa daga bikin kaddamar da wani dam da suka yi a gabar kasar da kasar Azerbaijan.

Daya daga cikin jami’an jirgin mai saukar ungulu da Raisi ke ciki ya tuntubi hukumar jiragen kasar bayan da jirgin nasu ya samu matsala.

Mohsen Mansouri mataimakin shugaban kasa kan harkokin zartarwa, ya ce. “Wannan yana daya daga cikin dalilan da suka sa ba mu yanke kauna da al’amarin ba. Muna fatan za su tsira.

Ya ce, “biyu daga cikin mutanen da ke cikin jirgin sun tuntubi mutanenmu a lokuta da dama.”

Ƙasar Turkiyya tuni ta tura jirage masu saukar ungulu masu fasahar bincike da dadddare domin taimakawa wurin neman shugaban kasar.

A lokacin, gwamnatin kasar Turkiyya ta ce “Mun aika da ma’aikata da motoci 6 da kwararru 32 zuwa Iran domin bayar da agaji wurin neman shugaban da ya faɗa da tsakanin tsaunuka.

“Gwamnatin Iran ta ce biyar daga cikin ’yan tawagar da muka tura suna daf da jirgin da ya bace.”