✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tsaro: Tinubu ya ƙaddamar da rundunar tsaron daji a faɗin Najeriya

Babban aikin rundunar shi ke fatattakar 'yan ta'adda da ke ɓuya a daji.

Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya amince da kafa sabuwar rundunar masu tsaron daji a faɗin ƙasar nan domin tinkarar matsalolin tsaro da ke ƙaruwa a cikin dazukan Najeriya.

A ƙarƙashin wannan sabon shiri, za a ɗauki sama da mutane 130,000 aiki da za su samu horo na musamman da kayan yaƙi na zamani domin kare dazuka guda 1,129 da ke sassa daban-daban na ƙasar nan.

Wannan na cikin wata sanarwa da mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan yaɗa labarai da hulɗa da jama’a, Sunday Dare, ya fitar a shafinsa na X.

Sanarwar ta bayyana cewa an amince da shirin ne a lokacin taron majalisar zartarwa ta tarayya da aka gudanar ranar Litinin.

A cewar sanarwar, shugaba Tinubu, ya umarci kowace jiha da ta ɗauki ma’aikata daga 2,000 zuwa 5,000 bisa ƙarfin kasafin kuɗinta, domin zama ’yan tsaron daji.

Ofishin mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan tsaro da ma’aikatar muhalli za su sanya ido a kan tsarin ɗaukar ma’aikatan da horar da su.

Babban aikin waɗannan masu tsaron dajin shi ne fatattakar ’yan ta’adda da miyagu da ke ɓuya a dazuka suna aikata laifuka.

Sanarwar ta ƙara da cewa Shugaba Tinubu ya bayyana buƙatar a bai wa masu aikin horo mai kyau da makamai na zamani domin kare rayuka da dukiyoyin ’yan Najeriya.