Wata ƙungiyar ’yan ta’adda mai alaƙa da ƙungiyar Alƙa’ida ta ɗauki alhakin kashe sojoji 200 a wasu jerin hare-hare a ƙasar Burkina Faso.
Ƙungiyar mai suna Jama’at Nusrat al-Islam wal-Muslimin (JNIM), ta ɗauki alhakin kai hari a Djibo, arewacin Burkina Faso, tana mai cewa ta kashe sojoji 200.
Wannan ikirarin, wanda cibiyar SITE Intelligence Group mai hedkwata a Amurka ta ruwaito a ranar Alhamis, ya biyo bayan iƙirarin JNIM na baya da ta yi na kashe sojoji 60 a harin.
SITE Intelligence Group, wacce ke sanya idanu kan ayyukan ƙungiyoyin masu tsattsauran ra’ayi ta intanet, ta nuna cewa harin wani bangare ne na ƙaruwar ayyukan JNIM a Burkina Faso a cikin watan da ya gabata, wanda ya haifar da asarar rayuka da dama.
- Ɗaukar fansa: Sojoji sun ragargaji Boko Haram a Dajin Sambisa
- An kama wata mata kan safarar makamai zuwa Katsina
Duk da cewa babu wani adadi na asarar rayuka a hukumance daga gwamnatin Burkina Faso, rahotanni sun ruwaito mazauna yankin Djibo sun nuna cewa an kashe sojoji da fararen hula da dama.
Sai dai, wata majiyar sojojin Burkina Faso, da take magana da Al Jazeera, ta nuna cewa ƙungiyar ’uan tayar da ƙayar bayan na iya aringizon da adadin waɗanda suka mutu.
Gwamnatin Burkina Faso har yanzu ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance kan harin ba.
Burkina Faso tana fama da ƙaruwar rikicin ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai a yankin Sahel.
Tun daga shekarar 2019, ƙaruwar tashe-tashen hankula ya raba sama da mutane miliyan da gidajensu, kuma ya nakasa muhimman ababen more rayuwa na farar hula, kamar asibitoci da makarantu.
Duk da alkawuran da gwamnatin mulkin soja, ƙarƙashin jagorancin Ibrahim Traore, ta yi na inganta yanayin tsaro da ƙulla sabbin ƙawance na tsaro da Rasha, ƙalubalen tsaro na ƙasar sun ƙara tabarbarewa a tsawon lokaci.
Burkina Faso ce ta kan gaba a jerin ƙasashe masu fama da ta’addanci na duniya (Global Terrorism Index) na shekarar 2024, inda ta zama kasa ta farko cikin sama da shekaru goma, baya ga Afghanistan ko Iraƙi, da ta mamaye matsayi na farko.
A shekarar 2023, kusan mutane 2,000 aka kashe a hare-haren ta’addanci 258 a ƙasar, wanda ya kai kusan kashi ɗaya cikin huɗu na mutuwar da ta shafi ta’addanci a duniya.