✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An Ninka Farashin Wutar Lantarki Sau 3 A Najeriya

Waɗanda ke karkashin tsarin Band A ne ke samun wutar lantarkin ta sa’o’i 20 a kullum.

Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Najeriya (NERC) ta amince da karin kudin wutan lantarki ga kwastomomin da ke karkashin rukunin samun wuta na Band A.

A wani taron manema labarai a wannan Larabar a Abuja, mataimakin shugaban NERC, Musliu Oseni, ya ce karin kuɗin zai mayar da kuɗin ma’aunin wutar lantarki na kilowatt ɗaya duk sa’a daga Naira 66 da ake biya a yanzu zuwa Naira 225.

Mun gano cewa waɗanda ke karkashin tsarin Band A ne ke samun wutar lantarkin na sa’o’i 20 a kullum.

Oseni ya ce wadannan kwastomomi suna wakiltar kashi 15 cikin dari na masu amfani da wutar lantarki miliyan 12 a kasar.

Ya kara da cewa hukumar ta sauke wasu kwastomomin da ke kan tsarin samun wuta daga Band A zuwa Band B.

Wannan ya zama wajibi ne saboda rashin cika sa’o’in da ake bukata na wutar lantarki da kamfanin rarraba wutar lantarkin ke samarwa.

“A halin yanzu muna da fidoji 800 da aka kasafta a matsayin Band A, amma yanzu za a rage su zuwa kasa da 500.

“Wannan yana nufin cewa kashi 17 ne cikin 100 suka cancanci zama masu amfani da matsotsar Band A.

A baya dai Kamfanin Dillancin Labarai na Bloomberg ya ce za a ba kamfanonin wutar lantarki damar kara farashin wutar lantarki zuwa N200 ($0.15) a kowace kilowatt daga naira 68 ga masu amfani da wuta a birane daga wannan watan.

Bloomberg ya bayyana hakan ne a ranar Talatar da ta gabata.

Ya ruwaito cewa, gwamnati ta ce waɗannan kwastomomi su ne masu wakiltar kashi 15% na al’ummar kasar da ke  amfani da kashi 40% na wutar lantarkin da ake samarwa.

Waɗansu majiyoyi daga fadar shugaban kasa da ke da masaniya kan lamarin sun ce za ayi hakan ne da nufin janyo hankulan sabbin masu zuba jari a harkokin wutar lantarki.

Wannan Tsarin Zai Karawa ‘Yan Najeriya Wahala

Masu fafutika kan inganta wutar lantarki a Najeriya sun bayyana wa wakilin mu cewa wannan lamari ya zo musu da kaduwa, inda suka ce, ba zai taba yiwuwa ‘yan Najeriya su jure matakin cire tallafin wutar lantarki kai tsaye ba, baya ga cire tallafin man fetur, lamarin da ya jefa rayuwar ‘yan ƙasar cikin tasku.

Da mu ka tuntubi Babban Manajan Hukumar kula da harkokin Jama’a a NERC, Dakta Usman Arabi a jiya, bai karba kiran mu ba kuma bai amsa sakonnin tes din mu ba.

Bloomberg ya ce Bayo Onanuga, mai magana da yawun fadar shugaban kasar ya ce, “Masu ruwa da tsaki a hukumar NERC za su yi wa ‘yan Najeriya jawabi idan sun kammala tattaunawa da kamfanonin rarrabawa da samar da wutar lantarki a ƙasar”.

Ya ce “Fadar Shugaban kasa ba zata iya cewa komai a kan wannan matakin ba. Bangaren wutar lantarki na cikin mawuyacin hali.”

An Takure ‘Yan Najeriya Da Yawa —Kungiyoyi

Mambobin ‘kungiyoyin fararen hula sun bayyana damuwarsu kan rahotannin baya-bayan nan da ke nuni da cewa gwamnatin tarayya na shirin rubanya farashin wutar lantarki kusan sau uku nan da ‘yan makwanni.

A nasa jawabin, babban daraktan Cibiyar Kula da ‘Yancin Dan Adam da Ilimin Jama’a (CHRIceD) Kwamared Ibrahim M. Zikirullahi ya bayyana cewa, kara farashin  kilowatt din wutar lantarki zuwa Naira 200, maimakon Naira 68 a halin yanzu a Najeriya na  nuna cewa gwamnatin Tinubu bata tausayin talakawan ƙasar nan.