✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan Sa-Kai Sun Kashe Masu Garkuwa Da Mutane 4 A Abuja

Wani manomi ne ya tsegunta musu cewa akwai masu garkuwa da mutane a yankin na Kuje da ke Abuja.

’Yan sa-kai sun harbe wasu mutane huɗu da ake zargi da ta’adar garkuwa da mutane a Abuja, babban birnin Nijeriya.

’Yan sa-kan da suka hada da ’yan banga da mafarauta sun kashe mutanen ne bayan bata kashin da suka tafka a dajin Yenche-Farakuti da ke Karamar Hukumar Kuje a ranar Alhamis ɗin da ta gabata.

An bayyana cewa al’ummar Yenche, mai tazarar kilomita biyu daga Farakuti, na iyaka da kananan hukumomin Kwali da Kuje na yankin.

Wani mafarauci da ke cikin tawagar da ta ragargaji waɗanda ake zargin, ya ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 11 na safe yayin da ‘yan banga da mafarauta ke sintiri na haɗin gwiwa tsakanin Yenche da Farakuti.

Ya bayyana cewa wani manomi ne ya tsegunta musu cewa akwai masu garkuwa da mutane a yankin.

Jin hakan ta sa ’yan banga da mafarautan da suka fito daga ƙauyukan Sabo da Agwe da Kwaku da kuma Yenche, suka gayyaci abokan aikinsu suka kutsa kai cikin dajin da sansanin masu garkuwa da mutanen.

Aminiya ta ruwaito cewa, bayan nan ne suka fara barin wuta a tsakaninsu har ta kai ga nasarar hallaka mutane huɗu daga cikin ’yan ta’addar.

Ya ci gaba da cewa, “Lokacin da muka isa sansanin, wasu daga cikinmu sun ɓoye kan bishiya, wasunmu kuma suka suka ja tunga, yayin da wasunmu kuma suka buɗe wuta kan masu garkuwa da mutanen, inda nan take suma suka maida martani da harbi mai tsanani.

“Bayan dan wani lokaci ne dai suka fahimci ba sarki sai Allah, wasu da suka yi saura suka ranta a na kare, huɗu daga cikinsu su kuma muka aika su lahira.”

Ya ce sun samu na’urorin sarrafa hasken rana zuwa lantarki, da tabarmi da igiya da kuma kayan abinci a sansanin ’yan ta’addan.

Kwamishinan ‘yan sandan Abuja, Benneth Igweh, ya tabbatar da faruwar lamarin a tattaunawar da muka yi da shi ta wayar tarho a ranar Talata.