Wani sabon rahoto kan matsalar tsaro da ta dabaibaye Nijeriya na tsawon lokaci ya nuna cewa yawan mutanen da ake kashewa a kullum a kasar ya zarce na wadanda ake yin garkuwa da su, kuma abin ya fi muni a jihohin Arewa.
Rahoton ya nuna cewa a kullum ana kashe akalla mutum 28, sannan an yi garkuwa da 24, inda aka kashe jimillar mutum 2,583 aka sace 2,164 a wata uku na farkon shekarar 2024 a kasa bai daya.
- Minista ya yi murabus saboda matsalar wutar lantarki a Saliyo
- An rufe kasuwanni saboda zaɓen kananan hukumomi a Oyo
Rahoton, wanda kamfanin Beacon Security and Intelligence Limited, – mai bincike kan matsalolin rashin tsaro – ya fitar, ya bayyana cewa kashe-kashe da sace-sace an fi yinsu ne a jihohin Arewa.
Rahoton kamfanin ya bayyana cewa daga watan Janairu zuwa Maris, kaso 80 cikin 100 na kashe-kashen da kuma kashi 94 cikin 100 na sace-sacen an yi su ne a jihohin Arewa.
Sai dai wannan rahoto ya ci karo da ikirarin da Mai bai wa Shugaban Kasa Shawara kan Harkokin Tsaro, Malam Nuhu Ribadu ya yi, inda ya bayyana cewa, matsalar tana raguwa kwarai da gaske a kasar nan.
Shi ma Ministan Tsaro kuma tsohon Gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Muhammadu Badaru Abubakar a farkon watan nan yayin wani taro na rundunar sojojin kasar nan, ya bayyana cewa ana samun nasara wajen yakin da ake yi da ta’addanci a Nijeriya.
Alkaluman kashe-kashe
Alkaluman da aka fitar sun nuna daga cikin mutanen da aka kashe a wata ukun farkon bana, 793 sun fito ne daga jihohin Arewa maso Yamma, sai 681 daga jihohin Arewa maso Gabas, sai 596 daga jihohin Arewa ta Tsakiya.
Wannan ya haɗa da hareharen ’yan bindiga, rikicin manoma da makiyaya da kuma rikicin kabilanci.
A Kudu maso Yamma kuma an kashe mutum 194, a Kudu maso Kudu kuma mutum 161, sannan a Kudu maso Gabas, wanda alkaluman suka nuna ya fi sauki, an kashe mutum 158.
Sannan kuma a Arewa aka fi samun rahotannin garkuwa da mutane domin karɓar kuɗin fansa.
Inda abin ya fi ƙamari Jihohin biyar da aka fi kashekashe su ne Borno 517, Binuwai 313, Katsina 252, Zamfara 212 sai kuma Kaduna 206.
Alƙaluman garkuwa da mutane
Rahotanni sun nuna cewa daga cikin mutum 2,164 da aka sace a cikin wata ukun farkon bana, an yi garkuwa da 1,297 a Arewa maso Yamma kadai.
An sace mutum 421 a Arewa maso Gabas, sai 330 a Arewa ta Tsakiya.
A Kudu maso Yamma kuma an sace mutum 30, Kudu maso Kudu 66, sai Kudu maso Gabas mutum 20.
Jihar Kaduna ta fi ko’ina yawan mutanen da aka sace da mutum 546 a wata uku na farkon 2024.
Sai Jihar Zamfara, in da aka sace mutum 447. An fi kashe mutane a Jihar Borno, amma kuma ita ce ta uku wajen satar mutane da mutum 340.
Sai Jihar Katsina, inda aka sace mutum 252 sannan Babban Birnin Tarayya, Abuja, inda a wata ukun farkon 2024 aka yi garkuwa da mutum 102 domin neman kudin fansa.
Akwai alamun nasara Sai dai duk da haka, masu sharhi a kan harkokin tsaro suna bayyana cewa akwai alamun nasara a yunƙurin dakile wannan matsala da ke neman zama ruwan dare.
Mai sharhi a kan harkokin tsaro, Yahuza Getso, ya bayyana cewa, yadda jami’an tsaro suka kara kaimi wajen fatattakar ’yan bindiga ya sa masu aikata laifuffuka sun yin hijirar dole, zuwa sababbin wurare don guje wa jami’an tsaro.
“Tunda jami’an tsaro suka mayar da hankali a kan ayyukansu a wuraren da suke da hadari, masu aikata laifuffuka kan yi kaura zuwa yankuna daban-daban,” in ji shi.
Ya ce, wannan gwamnatin tana sauraron shawarwari kan yadda za a shawo kan matsalar. Shugaban Kamfanin Kwararru kan Harkokin Tsaro na Beacon Consultants, Kabiru Adamu, a hirarsa da Aminiya ya danganta matsalar tsaro a Arewa da rashin ingantaccen tsarin shari’a da rashin kula da iyakoki da kuma yaduwar kananan makamai ba bisa ka’ida ba.
Ya ce, dimbin matasan da ba su da ilimi ko sanin makamar wani aiki da kuma tsarin shugabanci na kasa biyan bukatun ci gaban al’umma suna haifar da babban kalubale.
Adamu ya ce, za a iya shawo kan matsalolin tsaro a kasar nan ta hanyar hadin gwiwa tsakanin kungiyoyin tsaro, Gwamnatin Tarayya da gwamnatocin jihohi da kuma kasashe makwabta.
Ku gyara dangantarku da talakawa — Majalisar Dinkin Duniya ga shugabanni
Mataimakiyar Shugaban Majalisar Dinkin Duniya, Hajiya Amina Mohammed ta ce daya daga cikin hanyoyin da za a magance matsalar tsaro da ta addabi Afirka ita ce shugabanni su gyara huldarsu a tsakaninsu da talakawa, tare da samar da mulki mai inganci.
“Sake inganta dangantaka na da muhimmanci wajen farfado da amana. Wajibi ne mu ba da kula ga mata wadanda suka fi jin jiki daga ayyukan ’yan ta’adda, sai matasa.
“A tallafa musu a share musu hawayen ta’adancin da aka yi musu,” in ji ta a lokacin da take bayani a Babban Taron Afirka kan shawo matsalar rashin tsaro da aka yi a Abuja a ranar Litninin da ta gabata.
A jawabin Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu a wajen taron, ya yi kiran a samar da cibiyar yaki da ta’addanci ta nahiyar baki daya domin yaki da ta’addanci a iyakokin kasashen.
Ya ce cibiyar ce za ta rika tattarawa tare da raba bayanan sirri da yaki da ta’addanci a tsakanin kasashen Afirka.
Shugaban Kasar ya ce dole kasashen Afirka su dauki mataki mai kwari, musamman ta hanyar dauko aikin tun daga tushensa, kamar yaki da talauci da rashin adalci da rashin daidaito.
Ya ce, “Misali ku dubi yadda ake hakar ma’adinai ta barauniyar hanya yanzu.
“Duk wada yake tunanin hakar ma’adinai ta barauniyar hanya ba ta da alaka da ta’addanci bai fahimci lamarin ba.
“Dole ne kasashen waje su taimaka wajen kawo karshen wannan matsala saboda daga kasashen waje ne ake daukar nauyin ta’addancin nan, ba da kudaden Afirka ba.”
Shugaban Kasar ya nanata kudirin Nijeriya wajen aiki da duk wata kasar yankin domin yaki da safarar makamai da sauransu, sannan ya kara kira a sa ido sosai tare da kara kaimi wajen yaki da ta’addanci.
Tun farko, a jawabin maraba, Mai bai wa Shugaban Kasa Shawara kan Harkokin Tsaro, Malam Nuhu Ribadu ya ce akwai abubuwa da dama da suke ta’azzara matsalar tsaro a Afirka, inda ya ce daga ciki akwai talauci da rashin adalci da kuma daukar nauyin ta’addanci daga kasashen waje da sauransu.
Ya ce Nijeriya tana yi duk mai yiwuwa wajen daukar matakan da suka dace domin kawo karshen lamarin.