✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tinubu ya gana da shugabannin tsaro a Abuja

Shi ne karo na farko da Tinubun ke ganawa da jagororin tsaron tun bayan dawowarsa daga Faransa da Birtaniya.

Shugaban Ƙasa, Bola Tinubu ya gana da babban mai ba da shawara kan tsaron ƙasa, Nuhu Ribadu, da hafsan hafsoshin tsaro na ƙasa, Christopher Musa.

Rahotanni dai na nuna sun shiga taron ne a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja da misalin ƙarfe 3 na rana.

Wannan dai shi ne karo na farko da Tinubun ke ganawa da jagororin tsaron tun bayan dawowarsa daga Faransa da Birtaniya ranar Litinin.

Kafin dawowarsa dai, ‘yan siyasa da dama da sauran al’umma sun koka ka yadda shugaban ya shafe sati biyu a ƙasashen duk da cewa matsalar tsaro na ci gaba da tabarbarewa a tasa ƙasar.

Sai dai babu tabbacin cewa taron da shugabannin suka gudanar na da alaƙa da rikice-rikicen ko akasin haka.