Wani mutum da ake nema ruwa a jallo bisa zargin garkuwa da mutane an kama shi a sansanin alhazai da ke Abuja.
Wata majiya daga jami’an tsaro ta tabbatar wa wakilinmu cewa an kama wanda ake zargin, mai suna Yahaya Zango, yayin da ake tantance takardun maniyyatan da ke shirin tafiya Ƙasar Saudiyya domin aikin Hajjin bana.
- ’Yan sanda sun ceto tsohuwa mai shekara 80 a hannun ’yan bindiga a Jigawa.Shin PDP za ta iya ɗinke ɓarakarta nan da zaɓen 2027?
Rahotanni sun bayyana cewar Zango yana zaune ne a unguwar Paikon-Kore da ke cikin Ƙaramar Hukumar Gwagwalada a Babban Birnin Tarayya, Abuja.
Jami’an tsaro sun bayyana shi a matsayin wanda ake nema ruwa a jallo saboda zarginsa da hannu wajen garkuwa da mutane.
Majiyar ta ce mutumin ya zo da fasfonsa tare da sauran maniyyatan Abuja, amma jami’an hukumar DSS suka gane shi kuma suka cafke shi nan take suka tafi da shi.
Wani babban jami’i daga hukumar jin daɗin alhazai, ya tabbatar da kama shi, amma ya buƙaci a sakaya sunansa.
Rahotanni sun nuna cewa an daɗe ana nemansa kafin daga bisani aka yi nasarar cafke shi.
Da aka tuntuɓi kakakin rundunar ’yan sandan Abuja, SP Josephine Adeh, ta ce: “Ka ce DSS ce ta kama shi, amma ni kakakin rundunar ’yan sandan Abuja ce.”
DSS dai ba ta fitar da wata sanarwa kan lamarin ba har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto.
Kasancewar Najeriya na fama da matsalolin tsaro, hukumomi na ci gaba da ƙoƙarin magance su, duk da cewar har yanzu ana fama da barazanar hare-haren ’yan ta’adda.