Wani mutum ya mayar da wani littafin almara game da wata kasar kwatance mai taken George Orwell’s 1984, zuwa dakin karatun Amurka da ke Jihar Oregon bayan shekara 65.
A wani sako da ya rubuta kuma ya cusa a cikin littafin, mutumin mai shekara 86 wanda ya bayyana sunansa da WP kawai ya ce kamata ya yi ya mayar da littafin zuwa dakin karatu na Mulnomah da ke Portland saboda fa’idar da yake da shi har a zamanin yau.
“Bayan sake-karantawa karo da dama, na fahimci cewa, fiye da kowanne lokaci a baya, kamata ya yi a sake buga wannan littafi don samun sa a cikin jama’a,” rubutun ya ce.
Labarin almarar ya yi nuni ne da taken da ya shafi mulkin kama-karya da kuma tsage gaskiya.
“Ya kamata na mayar da wannan littafi ne a 1958, lokacin da nake shirin kammala karatu a [Jami’ar Jiha ta Portland], amma ban samu damar yin hakan ba,” ya rubuta a cikin sakon.
“A yi min afuwa kan wannan dogon jinkiri. A shekara 86, ina so a karshe na cire tunanin daga zuciyata,” in ji shi.
Mutumin ya ce a duk lokacin da ya sake karanta wani bangare na littafi, sai ya ji ya sake motsa masa kwadayin ya mayar da shi dakin karatun da ya ara.
”Muhimman sassan littafin har yanzu suna da tasiri kamar yadda suke da shi shekara 65 da ta wuce,” a cewarsa, inda takanas ya nunar da wani sashe a cikin shafi na 207.
“A takaicw ku kara kalmomin intanet da shafukan sada zumunta, za ku ji tamkar kuna karanta wani game da shekara ta 2023,” ya ce.
Littafin almarar wanda aka wallafa a 1949, an tsara shi ne a wata duniya inda gwamnatin kama-karya take murkushe tunanin tsage gaskiya.
Kasuwar littafin ta bude a Amurka cikin 2017 jim kadan bayan wani babban mai ba da shawara ga Donald Trump, wanda shi ne Shugaban Kasa a lokacin, ya ce Fadar White House na fitar da “bayanai masu shigen gaskiya” a wani rikici game da girman taron mutanen da suka halarci bikin rantsar da shi.
Da yake mayar da martani ga littafin da aka mayar, Dakin Karatu na Multnomah County ya ce ba za a ci mutumin tara a kan mayarwar a makare ba.
BBC