Bayan sake sanya hannu kan yarjejeniyar dakatar da kai wa juna hare-hare a Sudan, an zargi bangarorin da ke rikici a kasar da sake yin watsi da batun mai muhimmanci.
Kasashen Amurka da Saudiyya, sun ce suna bincike kan bayanan da ke nuna cewa bangarorin kasar Sudan da ke yaki da juna, sun saba yarjejeniyar nan ta tsagaita wuta da suka cimma a baya-bayan nan.
- Gwamnan Kwara ya zama sabon Shugaban Kungiyar Gwamnoni
- WhatsApp ya bullo da tsarin gyara saƙon da aka aika — Zuckerberg
Wannan na zuwa ne yayin da ake kokarin fara aikin samar da agajin jinkai gadan-gadan a Sudan din.
Cikin wata sanarwa ta hadin gwiwa, kasashen biyu da ke kai komon ganin an sasanta rikicin na Sudan, sun ce bangarorin ba su mutunta abin da aka amince da shi na cewa babu batun afka wa juna tun ma kafin yarjejeniyar ta fara aiki a ranar Litinin.
Kwamitin da ke sa ido kan tsagaita wutar dai, ya fada a jiya Talata cewa a binciken da ya gudanar ya gano yadda aka yi fatali da abun da aka tsaya a kai game da dakatar da kai wa juna hare-haren.