✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

WhatsApp ya bullo da tsarin gyara saƙon da aka aika — Zuckerberg

An kirkiri wannan aikin don habaka daidaito da tsabtar sadarwa.

Shahararrren kamfanin aika sako na nan take na WhatsApp, ya sanar da wani tsari wanda zai bai wa masu amfani da manhajar damar gyara saƙonnin da suka aika da su.

Mark Zuckerberg, babban mamallakin na Kamfanin Meta ya bayyana wannan sabon ci gaban cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

A wannan sabon fasalin, yanzu masu amfani da WhatsApp za su iya gyara sakonnin da suka aika har bayan mintuna 15 bayan aika su.

A baya can, masu amfani dole ne su bi wasu hanyoyin kamar share sakon ko sake aika sako na biyu a matsayin gyara.

Fasalin gyarar sakon yana nufin samar wa masu amfani da manhajar Whatsapp karin iko a tattaunawarsu, ba su damar gyara kurakurai, yin bayani, ko kara muhimman bayanai cikin sakonsu.

“Cikin hanya mai sauki ake amfani da tsarin gyaran sako na Whatsapp, za su iya danna ko kuma rike takamaiman sakon da suke son gyarawa. Menu zai bayyana, yana gabatar da zabi mai dauke da sakon “Edit”. Sai a zaba wannan zabi, ana zabansa za a sami damar yin gyara abubuwan sako daidai biyan bukata.

“An kirkiri wannan aikin don habaka daidaito da tsabtar sadarwa, bai wa masu amfani damar gyara kurakurai ko samar da karin bayani cikin sauri.

“Aiwatar da fasalin gyarar sakon yana nuna kudurin WhatsApp don habaka kwarewar mai amfani gaba daya. Ta hanyar karfafa masu amfani da manhajar ikon gyara sakonnin da aka aika, WhatsApp yana da nufin magance matsalolin gama gari na kurakurai ko canje-canje a yayin tattaunawa a cikin manhajar.

Meta, babban kamfani na WhatsApp, ya nuna sha’awar sabon fasalin kuma ya jaddada cewa masu amfani za su sami karin iko akan tadi da gyara kuskuren haruffa.

An riga an fara fitar da fasalin gyarar sakon, kuma tuni mafiya yawan masu amfani da manhajar sun fara cin moriyar wannan sabon fasali kuma kamfanin na Meta ya tabbatar da na ba da jimawa ba dukkannin masu amfani da manhajar za su sami damar amfani da wannan sabon fasali.

Yana da kyau a lura cewa sauran manhajoji na aika sako, kamar Telegram da Signal, sun riga sun ba da damar gyara sakonni iri daya ga masu amfani da su.

Bugu da kari, masu amfani da manhajar Twitter wanda ake biya sun dade su na iya samun dama ga maballin gyara don yin canje-canje ga sakon tweets dinsu.

VOA