✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An kwantar da daliban firamare 18 a asibiti bayan cin abincin makaranta

An kwantar da daliban wata makarantar firamare su 18 a asibiti bayn da suka ci abincin da Gwamantin Jihar Osun take ciyar da dalibai a…

An kwantar da daliban wata makarantar firamare su 18 a asibiti bayn da suka ci abincin da Gwamantin Jihar Osun take ciyar da dalibai a makarantu.

Kmisihinan yada labaran jihar, Kolapo Alimi ya ce gwamnan jihar, Ademola Adelek ya ba da umarnin gudanar da bincike a kawo masa rahoto kan abin da ya faru.

Baya ya bayyana cewa daga baya an sallami yaran daga asibitin bayan da sun samu sauki.

Alimi ya ce Gwamna Adeleke ya ba da umarnin dakatar da shirin ciyar da dalibai a makarantar da abin ya faru.

Wannan abu dai ya faru ne a makarantar St. James B, Owo-Ope da ke Osogbo, babban birnin jihar.

Kwamishinan ilimin ya ce an gayyaci mai girkin abinci a makarantar zuwa gidan gwamnati, inda aka ba da umarnin tabbtar da ingancin abicin da ake ba wa dalibai.

Gwamnatin jihar ta kuma ziyarci iyayen daliban tare da biyan kudin asibitinsu na jinyar.