✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hayaniya ta kaure a Majalisar Kano kan kudaden masarautu

Majalisar Dokokin Kano ta amince da karamin kasafin 2023 na Naira biliyan 24

An tayar da jijiyoyin wuya a zauren Majalisar Dokokin Kano, kan kudaden da gwamnatin jihar ta ware wa masarautu a karamin kasafinta na 2023.

Takaddamar ta kaure ne a yayin zaman tantance kwarya-kwaryan kasafin kudi na Naira biliyan 24 da Gwamna Abba Kabir ya gabatar domin amincewar majalisar.

A yayin bibiyan kasafin ne ’yan majalisa suka diga alamar tambaya bayan da suak ga an ware masarautan Kano, Gaya, Rano da Bichi Naira miliyan 2.5 kowannensu, amma aka ware wa Masarautar Karaye Naira miliyan 50 a cikin kasafin.

A yayin hayaniyar ne shuugaban majalisar, Jibrin Falgore, ya bayyana wa mambobi cewa Masarautar Karaye ce kadai ta kare kasafin da aka ware mata a cikin masarautu biyar da ke jihar.

Bayan bayanin da shugaban majalisar ya yi musu ne kurar ta lafa.

Majalisar Kano ta amince da karamin kasafin N24 na 2023

A karshen zaman dai, Majalisar ta amince da karamin kasafin kudin na karin Naira biliyan 24 a kan kasafin  jihar na shekarar 2023.

Amincewar majalisar da kwarya-kwaryan kasafin da Gwamnan ya gabatar mata ya kara yawan kasafin jihar na 2023 zuwa biliyan 350.

A watan da ya gabata ne gwamnan ya gabatar da kwarya-kwaryan kasafin a gaban wa majalisar domin amincewarta.

Shugaban Masu Rinjaye kuma dan majalisa mai wakiltar Dala, Lawan Hussaini (NNPP) ya ce kwarya-kwaryan kasafin kudin zai ba wa gwamnatin jihar damar aiwatar da manyan ayyuka a bangaren ilimi da na kiwon lafiya.

Baya ga haka, gwamnatin za ta samu zarafin biyan kudaden giratuti da fanshon ma’aikatanta da suka yi ritaya.