Ilimi na da muhimmanci wajen gina al’umma, amma ga daliban Makarantar Firamare ta Bare a karamar Hukumar billiri, Jihar Gombe, wannan lamari ya zama kamar mafarki mai wahalar tabbatuwa.
Duk da ikirarin da Gwamnatin Jihar Gombe ke yi na cewa, tana fifita ilimi ta hanyar manyan ayyuka kamar gine-ginen makarantu masu hawa biyu a kowace mazabar Sanata, a halin da ake ciki a Makarantar Firamare ta Bare ba ta san da hakan ba. Wannan makaranta tana nuna sakaci da gazawar masu mulki.
An kafa makarantar ce a shekarar 2005 karkashin shirin Hukumar Kula da Ilimin Firamare ta Jihar Gombe (SUBEB). Tun daga lokacin har zuwa yanzu, ba a taba samun gyara ko ci-gaba ba. Maimakon zama alamar ci-gaba, makarantar ta koma kamar wani gida da aka watsar.
Wakilinmu ya yi tattaki zuwa wannan makaranta da take cikin mummunan yanayi. Ban da ofishin shugabar makarantar, babu wani dakin karatu a makarantar da ke da kofofi ko tagogi ko sili mai kyau.
Dalibai suna zama ne a kasa, saboda babu kujeru da tebura ko kayan karatu na zamani. Malamai kuma na fama da irin wannan matsa, wadda take hana su bayar da ingantaccen ilimi.
Makarantar tana da azuzuwan karatu biyu ne kadai a gini daya da kuma wani gini da aka ba su aro, daga bisani aka mallaka wa makarantar, wanda shi ma ya lalace, babu kofofi babu tagogi.
A halin yanzu, makarantar na da dalibai sama da 400, adadi mai yawa idan aka kwatanta da karancin kayan aiki da take da su.
Don shawo kan wannan matsala, ana hade daliban firamare na Aji 1A, 1B, da 1C cikin aji daya. Wannan cunkoso ya sa koyarwa da karatu suka zama cikin mawuyacin yanayi.
Wani dalibi ya bayyana cewa, “saboda mu ‘ya’yan talakawa ne, gwamnati ba ta damu da gyara makarantarmu ba. Da iyayenmu suna da hali, da sun kai mu makarantu masu inganci.”
Wannan kalamai sun bayyana halin da marasa galihu ke ciki, inda makomarsu take fuskantar barazana saboda rashin kulawar gwamnati.
Bugu da kari, al’ummar unguwar sun kasa tashi tsaye wajen neman gyara makarantar,
sai dai wani mazaunin garin ya ce, gyaran azuzuwan makarantar ba zai bukaci kudade masu yawa ba. Amma duk da haka, kusan shekara 20 ke ann ba tare da wani yunkurin gyara ba.
Da wakilinmu ya nemi jin ta bakin Kwamishiniyar Ilimi ta Jihar Gombe, Hajiya Aishatu Umar Maigari, sai ta ce, makarantar ba a karkashinta take ba, tana karkashin Hukumar SUBEB ce don haka SUBEB za a tuntuba, ita ba ta da ta cewa a kai.
Da muka tunubi Sakataren SUBEB, Babaji Babadidi ta wayar salula, ya bayyana cewa, bai san halin da makarantar ke ciki ba, domin bai da cikakken rahoto a kanta kasancewar a tunaninsa wai makarantar almajirai ce saboda lalacewarta.
Amma ya jinjina wa wakilinmu na ankarar da shi da ya yi kan yanayin da makarantar take ciki, inda ya yi alkawarin bincike tare da hadin gwiwar Sakataren Ilimi na karamar Hukumar billiri.
Yanayin Makarantar Firamare ta Bare na nuna rashin daidaito cikin tsarin ilimi a Gombe. Duk da ikirarin da gwamnati ta yi na inganta ilimin firamare, makarantu irin su Bare na ci gaba da kasancewa cikin halin kaka-naka-yi.
Ya kamata gwamnati ta gaggauta gyaran makarantar, ta samar da kayan aiki da kuma daukar karin malamai. Hakazalika, al’ummar yankin ya zama wajibi su tsaya tsayin daka wajen sa ido kan hukumomi domin ganin an samu ci gaba mai dorewa.
Daliban makarantar sun fi bukatar ganin gyara fiye da alkawuran da ba a cika su ba, domin suna bukatar makoma mai kyau ta hanyar samun ingantaccen ilimi, ba wanda ake lalatawa ba saboda sakaci.
Koken iyaye kan matsaloli da bukatar gaggauta gyaran makarantar
Malam Yusuf Abdullahi, tsohon malamin makarantar da yanzu ke aiki a wani wuri daban, ya bayyana cewa, malamai suna iyakar kokarinsu duk da mawuyacin yanayin da suke fuskanta.
Ya ce, yaransa biyu suna karatu a makarantar, suna kokari a bangaren karatu, amma rashin kujeru da kayan koyarwa yana rage wa dalibai sha’awa.
“Yara suna zama ne a kasa yayin darussa, wasu kuma suna barin makarantar gaba daya saboda munin yanayin karatun,” in ji Yusuf cikin damuwa.
Ya kara da cewa, wasu iyaye na cire ‘ya’yansu zuwa makarantu masu kayan aiki, irin su Central Primary School ko Ibinola, inda yanayin karatu ya fi inganci.
Malama Maryam Shu’aibu, mahaifiyar yara uku da ke karatu a makarantar ta bayyana takaicinta, “ina son mayar da ‘ya’yana wata makaranta, amma rashin kudi ya hana ni. Kodayake ba mu biyan kudin makaranta, sai dai Naira 200 na kudin PTA, amma makarantar ba ta da muhimman kayan aiki,” in ji ta
Ta roki gwamnati da ta samar da kujeru da littattafai da sauran kayan koyarwa domin tabbatar da yara na samun yanayin karatu mai kyau kafin su shiga makarantar sakandare.
Ita ma Shugabar makarantar, Misis Talatu Idi, ta bayyana halin da ake ciki a makarantar cikin bakin ciki. “Makarantar ba ta da kujeru da tagogi da kofofi, har ma da rufin kwano mai kyau a dakunan karatu. dalibai na zama a kasa, suna korafin kullum kayansu suna datti da ta sa wasu ba sa zuwa makarantar.
A wasu lokuta, mutanen gari suna yin bayan gida a cikin dakunan karatun makarantar, sai yara sun fito karatu a sa su kwashe, saboda rashin kofofi da tagogi da cikakken tsaro a makarantar, wanda hakan ke kara tabarbarbara yanayin makarantar’’.
Misis Talatu ta kara da cewa, kayan koyarwa sun yi karanci, kuma ita take biyan mai musu gadin makarantar a aljihunta Naira dubu 3,000 wani lokaci 2,500 saboda babu wani tanadi daga kasafin kudin gwamnati.
Hakimin Bare, Galadiman Tangale, Alhaji Yunusa Adamu Galadima, wanda shi ne Shugaban Hukumar Makarantar (SBMC) ya ce, an sha kokarin ganin an gyara makarantar, amma ba a samu nasara ba.
Ya ce, sun rubuta takardu zuwa hukumomin da abin ya shafa, ciki har da SUBEB da sashen ilimi na karamar hukuma, amma ba tare da wani sakamako ba.
Acewarsa, yana zargin ko idan aka tashi gyaran makarantar ana karkatar da aikin zuwa wani waje ne ba su sani, domin akwai wata makaranta mai suna BORE su kuma BARE ne, sunansu ya yi kama da Bare. wanda tun bayan gina azuzuwan farko guda biyu har yanzu ba a sake aza tubali ko wane iri ba.
Da muka tuntubi Sakataren Ilimi na karamar Hukumar billiri, Mista Titus Ladoji ya tabbatar da cewa, makarantar ba ta taba samun gyara ba tun da aka gina ta a 2005.
Ya yarda cewa, Makarantar Firamare ta Bare tana cikin makarantu da ke cikin mawuyacin hali, amma ba a sa ta cikin jerin makarantun da za a gyara ba tukuna.
Duk da kokarin da hakimin ya yi na samar da fitilu a makarantar, domin hana sata da lalata kayan makarantar, yanayin makarantar yana bukatar daukar matakin gwamnati na gaggawa.