Gwamnatin Jihar Gombe ta sanya hannu kan yarjejeniyar Naira biliyan uku domin gina mayankar dabbobi ta zamani a garin Gombe.
Hakan wani bangare ne na shirin inganta kiwon dabbobi da tsaftar abinci da kuma rage matsalolin kiwon dabbobi (L-PRES) wanda Bankin Duniya ke tallafa wa. Shirin L-PRES na da nufin kyautata harkar kiwon dabbobi da sarrafa nama cikin tsafta a jihar.
An kulla yarjejeniyar ce tare da kamfanin Lubel Nigeria Limited da wa’adin kammalawa na watanni 9, zuwa watan Fabrairun shekarar 2025.
An gudanar da bikin sanya hannu kan yarjejeniyar a ofishin L-PRES da ke G.R.A, a Gombe, inda shugaban shirin na jihar, Farfesa Usman Bello Abubakar, ya bayyana wannan aiki a matsayin babban ci-gaba a jihar.
“Wannan ba kawai wurin yanka dabbobi ba ne, amma zuba jari ne ga ci-gaban kiwon dabbobinmu. Za mu tabbatar da aiki da ka’idojin duniya wajen tsafta, yanka, da sarrafa nama,” in ji shi.
Farfesa Abubakar ya kuma yaba wa Gwamna Inuwa Yahaya saboda hangen nesansa wajen kyautata kayan more rayuwa da bunkasa tattalin arzikin jihar.
Shugaban gudanarwa na kamfanin Lubel Nigeria Limited, Akitet Yunusa Yakubu, ya yi alkawarin kammala aikin cikin inganci da kuma a kan lokaci, tare da alkawarin cika dukkan sharudda domin tabbatar da nasarar aikin.
Da zarar an kammala wannan mayankar dabbobi na zamani, ana sa ran zai kawo sauyi mai amfani ga harkar sarrafa nama a Jihar Gombe, da rage hadarin rashin tsafta da ke tattare da hanyoyin gargajiya, tare da samar da damammaki a cikin darajar kiwon dabbobi.