✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kori karen Joe Biden daga White House saboda yawan cizon mutane

Sai dai ba a san ko za a dawo da karen a nan gaba ba, ko a'a

An fitar da karen Shugaban Amurka, Joe Biden, daga fadar gwamnatin kasar ta White House saboda yadda yake yawan cizon mutane.

Mai magana da yawun uwargidan shugaban, Jill Biden, wato Elizabeth Alexander, ta ce daukar matakin ya biyo bayan yadda karen mai suna “Commander” ya ciji wani ma’aikacin fadar da kuma wasu ma’aikatan hukumar leken asirin kasar.

Elizabeth, a cikin wata sanarwa a ranar Laraba ta ce shugaban da maidakinsa sun damu matuka da lafiyar ma’aikatan da kuma jami’an tsaron da suke kula da su.

“Yanzu haka Commander ba ya cikin fadar, a daidai lokacin da ake ci gaba da nazari a kan mataki na gaba da za a dauka.

“Biden da maidakinsa suna matukar godiya saboda hakuri da goyon bayan da Hukumar Leken Asirin Amurka da dukkan wadanda abin ya shafa suka nuna, yayin da suke ci gaba da kokarin lalubo bakin zaren,” in ji Elizabeth.

Sai dai ba ta bayyana inda aka kai karen ba mai shekara biyu, wanda aka horar a kasar Jamus, sannan ba ta fadi ko matakin na wucin gadi ne ko kuma na dindindin ba.

Tun ranar Asabar din da ta gabata dai rabon da a ga karen, inda a ranar aka hange shi a saman wani ginin da shugaban yake zama.