✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Da takardun wani bakin Ba’amurike Tinubu yake amfani – Lauyan Atiku

Ya ce hatta wasu daga cikin takardun Tinubu sun nuna shi mace ne

Kalu Kalu, daya daga cikin lauyoyin dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar PDP a zaben 2023, Atiku Abubakar, ya ce sun gano takardun karatun da Shugaban Najeriya Bola Tinubu ke amfani da su na wani bakin Ba’amurike ne.

Ya bayyana hakan ne yayin wani taron manema labarai da tsohon Mataimakin Shugaban Kasar ya shirya ranar Alhamis a Abuja.

Yana tsokaci ne a kan maganar da Jami’ar Jihar Chicago da ke Amurka ta yi cewa takardun da Tinubu ya gabatar wa Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) a zaben da ya gabata ba daga wajensu suke ba.

A cewar lauyan, “Daya daga cikin takardun karatun da jami’ar ta fitar ga lauyoyin Alhaji Atiku Abubakar, sun nuna ya yi takardar ce ta bogi.

“Na biyu kuma takardar kwalejin Southwest da ke Chicago wacce jami’ar ta yi amfani da ita wajen ba shi gurbin karatu, ta nuna mai takardar mace ne. Hakan ke nan na nuna cewa takardar ba ta Atiku ba ce.

“Sannan na uku, takardar neman shiga jami’ar da Tinubu ya gabatar wa kotun ta nuna ya shiga Kwalejin Gwamnati da ke Legas, sannan ya gama ta a 1970, amma a zahirin gaskiya ma sai a shekarar 1974 aka kafa makarantar.

“Wannan takardar kuma ta nuna mamallakinta wani bakin Ba’amurike ne, alhalin a fom din da ya mika wa INEC, ya musanta cewa yana da takardar zama dan wata kasar ban da Najeriya, wanda hakan ke nufin ke nan takardar ba ta shi ba ce.”