✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kashe mutum 222, an yi wa 20 fyade a wata 3 a Kaduna – Rahoto

An dai sami alkaluman ne daga jami'an tsaro.

A Jihar Kaduna a kalla mutum 222 ne ’yan bindiga suka kashe tare da yi wa mata 20 fyade, ciki har da karamin yaro daga tsakanin watannin Afrilu zuwa Yunin 2021.

’Yan bindigar sun kuma yi garkuwa da mutum 774, sannan sun raunata 226, ciki har da mata da kananan yara.

  1. Majalisa na neman a daina ba ’yan kasa da shekaru 16 gurabe a jami’o’i
  2. Buhari zai gana da duk Sanatoci 109 a daren Talata

Hakan na kunshe ne a cikin wani rahoton sha’anin tsaro da Kwamishinan Tsaro da Al’amuran Cikin Gida na Jihar, Samuel Aruwan, ya gabatar kan matsalar tsaro a Jihar.

A cewar rahoton, mutum 159 daga cikin wadanda aka kashe sun fito ne daga shiyyar Kaduna a tsakiya; wanda ya kunshi Kananan Hukumomin Birnin Gwari, Giwa, Igabi, Chikun da kuma Kajuru.

Ya kara da cewar, mutum 54 da aka kashe kuma sun fito daga yankin kudancin Kaduna; da ya Kananan Hukumomin Jema’a, Kachia da kuma Kauru.

Amma yankin arewacin Kaduna mutum tara ne suka rasa rayukanus a hannun ‘yan bindiga a  tsawon lokacin.

Har wa yau, Kwamishinan ya ce daga cikin mata 239 da aka yi garkuwa da su, 32 yara ne.

Shiyyar Kaduna ta tsakiya dai a cewar rahoton na da adadin mutum 555 da aka sace, yayin da Kaduna ta arewa ke da mutum 55.

Kazalika, ya ce a tsawon lokacin, jami’an tsaro sun kashe ’yan bindiga 87 sannan Sashen Bincike na Musamman na Hukumar Tsaron Farin Kaya ta DSS sun cafke mutum 24 kan zargin ayyukan ta’addanci.

“’Yan bindiga sun yi wa mata 20 fyade, ciki har da kananan yara ’yan kasa da shekara 18, tare da yaro mai shekara bakwai a duniya a Karamar Hukumar Kudan,” a cewarsa.

Aruwan, ya kuma ce kimanin shanu 8,53 ne ’yan bindiga suka yi awon gaba da su a tsawon watannin.

Kwamishinan ya ce hare-haren sun jefa rayuwar mutane da dama a yankunan cikin barazana, lamarin da ya tilasta musu tserewa daga gidaje da gonakinsu, don gudun yin garkuwa da su.

Ya ce an sami alkaluman ne daga jami’an tsaron jihar.