Wasu ’yan uwa uku da suka hada sun shiga komar ’yan sandan Jihar Ogun bisa zargin kashe wani mai gadi a ranar jajibirin Kirsimetin da ta gabata.
Rundunar ’yan sandan jihar ta kame ’yan ukun ne a ranar Kirisimeti bayan da suka yi wa mai gadin dukan kawo wuka, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwarsa.
- Tsoron iyayenmu na hana maza neman aurenmu —’Yan matan barikin soja
- An kama kwarto ya haka ramin da ke kai shi gidan auren tsohuwar budurwarsa
- Mata dubu: An daure mai wa’azi shekara dubu
- Zaben Kano: Akwai alamun nasara a duk kananan hukumomi —Ganduje
Mai magana da yawun rundunar ’yan sandan Jihar Ogun DSP Abimbola Oyeyemi ya shaida wa Aminiya cewa, daya daga cikin ’yan uwan ukun na yin sana’ar tukin babur na acaba ne.
A lokacin da lamarin ya auku mai yin acabar ya dauko fasinjoji biyu a kan babur, ya yi yunkurin shiga rukunin gidajen da ke yankin Asero a Abeokuta inda mai gadin ke aiki, lamarin da ya sa masu gadin biyu da ke aiki a lokacin suka hana shi shiga domin dokar da ta yi hani da yin goyon fasinjoji biyu a babur a cikin rukunin gidajen.
Hakan ne ya sa dan acabar ya kira karin ’yan uwansa biyu suka rufar wa masu gadin da duka har daya daga cikinsu mai suna Segun Godfrey Barde ya mutu a asibiti, bayan da aka garzaya da shi asibitin a sume.
Ya ce, Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Ogun, CP Edward Ajogun ya ba da umarnin tasa keyar wadanda ake zargin zuwa Sashen Binciken Manyan Laifuka na rundunar, yayin da aka kai gawar mamacin dakin ajiyar gawa domin ci gaba da bincike.