Sojoji sun tsare wasu ’yan mata uku ’yan talla kan zargin kai wa ’yan bindiga bayanai a yankin Dogon-Daji a Karamar Hukumar Kagarko, Jihar Kaduna.
Wani mazaunin garin, Yakubu Ishaku, ya ce a ranar Alhamis sojoji suka kawo wani samame suka kama mata ’yan talla su uku a kauyen Kadara.
Ya ce ’yan matan da ke tallar zuma, an kama su ne bayan bayanan sirri da sojojin suka samu daga wani mai kai wa ’yan bindiga bayanai da sojoji suka kama yankin makonni biyu da suka gabata.
Wani basaraken yankin da ya bukaci a boye sunansa ya tabbatar da kama ’yan matan su uku.
- An ceto ’yar shekara 2 da maƙocinsu ya sace ta a Kano
- Yadda ’yan bindiga suka kashe sojoji 5 suka kona motarsu a hanyar Abuja
A cewarsa, “Gaskiya ne sojoji sun kama wasu ’yan mata uku ’yan talla a yankin kauyen Dogon-Daji a makon jiya.
“Na yi mamakin ganin cewa ’yan talla da ke sayar da zuma za su kasance masu kai wa ’yan bindiga bayanai.”
A baya-bayan nan jami’an tsaro sun kama ’yan bindiga a yayin wani samame a kauyen SCC da ke kusa da kasuwar garin Jere.
Aminiya ta gano cewa kasuwar kauyen SCC na samun tururuwar masu kasuwancin dabbobi da citta da sauran kayan abinci a yankin.
Wakikinmu ya yi kokarin samun karin bayani kan kama ’yan matan daga kakakin ’yan sandan Jihar Kaduna, ASP Hassan Mansur, amma hakan bai wa samu ba.