✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda ’yan bindiga suka kashe sojoji 5 suka kona motarsu a hanyar Abuja

Yankin Audu Jangwam ya yi kaurin suna da ayyukan ’yan fashi da masu garkuwa da mutane

’Yan bindiga sun kashe sojoji biyar tare da kona motarsu a yankin Audu Jangwam da ke kan hanyar zuwa Abuja a Jihar Kaduna.

Wani basarake a yankin da ya nemi a boye sunansa ya ce ’yan ta’addan sun harbe sojojin har lahira ne a wani harin kwanton bauna.

Ya shaida wa wakilinmu ta wayar salula cewa abin ya faru ne da misalin karfe 6 na yammacin ranar Alhamis a yankin da ke kusa da Sansanin Alheri Camp a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja.

Ya bayyana cewa, “’yan bindigar sun kai harin kwanton bauna ne kan sansanin sojoji, inda suka kashe mutane biyar suka kona motarsu.

Yankin Audu Jangwam ya yi kaurin suna da ayyukan ’yan fashi da masu garkuwa da mutane

Sojoji sun kwato shanun sata 162

Wakilinmu ya kuma samu labarin cewa a ranar Asabar din da ta gabata ne sojoji suka kwato shanun sata 162 a yayin samamen da suka yi maboyar ’yan bindiga a dajin Iche da ke karamar hukumar Kagarko.

Wani mazaunin garin, Sama’ila Adamu, ya ce an sace shanun ne a wata rugar Fulani makonni biyu da suka gabata.

Kakakin rundunar ’yan sandan jihar Kaduna, ASP Hassan Mansur, bai tabbatar da faruwar lamarin ba.