Wani mutum ya shiga hannu bayan da ya sace wa wani fasinja Naira miliyan daya a yayin da suke tafiya a jirgin kamfanin Air Peace.
Dubun barawon ta cika ne a hanyar jirgin na zuwa Fatakwal daga Abuja a ranar Laraba 27 ga watan Yuli, 2023, kwanaki kadan bayan an kama fasinjar kamfanin jirgi na Ibom Air ta sace wa wani fasinja kwamfutarsa, laptop.
- Yanzu-yanzu: Masu Zanga-Zangar cire tallafin mai Sun Ɓalle Ƙofar Majalisa
- DAGA LARABA: Abin Da Ya Sa Muke Yin Ciko —’Yan Mata
Kakakin kamfanin Air Peace, Stanley Olisa, ya ce fasinjar ta sace kudin da ke ajiye a cikin wata ambula ne, amma mai kudin ya kama ta dumu-dumu, ya kuma sanar da ma’aikatan jirgin.
Olisa ta ce, barauniyar ta sace kudin ne bayan da, “ta dauki jakar kwamfutar wani fasinja da ke aje a akwakun sama jirgi, ta cire ambulan din da kudin (Naira miliyan daya) ke ciki, sannan ta sanya kwamfutar a wani akwaku na daban, ta je ta zauna a wani kujera da babu kowa a bayan jirgin.
“Yana cikin wadan da suka yi saurin fita daga jirgin sabanin tsarin fita da ma’aikata suka sanar, amma aka kama shi, aka kwace kudin. An kuma same shi da dauke da kudaden kasashen daban-daban”.
An dai mika shi ga jami’an tsaro na Hukumar Kula da Filayen Jiragen Sama (FAAN) domin damka shi a hannun ’yan sanda du gudanar da bincike.
’Yan sanda sun sanar cewa an sake shi bayan ba da belin sa, kuma da wuya a gurfanar da shi, saboda mai kudin ya nuna ba ya son hakan.