✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sibil Difens ta cafke mutum 17 kan aikata sata a Yobe

Kwamandan ya ce za a gurfanar da su a gaban kotu da zarar sun kammala bincike.

Hukumar Sibil Difens (NSCDC), a Jihar Yobe, ta kama wasu mutum 17 da ake zargi da satar kayayyakin lantarki da na’urorin sadarwa a jihar.

Kwamandan rundunar, AS Dandaura, ya tabbatar da kamen a Damaturu, Babban Birnin jihar, inda ya ce an gano wuraren ajiya uku da ake amfani da su don ɓoye kayan sata.

Ya bayyana cewa samamen da aka kai ya taimaka wajen gano wuraren ajiya guda uku—ɗaya a kusa da ofishin Hukumar Alhazai a Damaturu, na biyu a Duriya bayan sabuwar kasuwa, sai kuma na uku a Abbari bypass.

Dandaura ya ce an kama shugaban wata ƙungiyar dillalan kayayyakin bola a yankin, Aliyu Ajakuta, wanda ake zargi da jagorantar aikata satar.

Haka kuma, an cafke wasu da ake zargi da hannu a laifin, ciki har da Umar Sai’adu mai shekara 17, Mohammed Salisu mai shekara 25.

Sauran sun haɗa da Ali Adam mai shekara 18, Ibrahim Mohammed mai shekara 19, Mohammed Musa mai shekara 20, Abdulhamid Mohammed mai shekara 15 da Hassan Dauda mai shekara 18.

Sauran da aka kama sun haɗa da Alhassan Yakubu mai shekara 26, Mohammed Babagana mai shekara 29, Mohammed Bashiru mai shekara 18, Mohammed Bello mai shekara 17, Adamu Abdullahi Usman mai shekara 20, Mustapha Babagana mai shekara 23, Tijani Bako mai shekara 19, Bashiru Adam mai shekara 18 da Lawal Salisu mai shekara 19.

Hukumar ta bayyana cewa ta ƙwato kayayyaki masu yawa daga hannunsu, ciki har da na’urorin sadarwa, igiyoyi masu sulke, manyan karafunan titin, farantin sola, batura, da sauran kayayyaki.

Kwamandan ya jaddada cewa za a gurfanar da waɗanda ake zargi a gaban kotu bayan kammala bincike.