✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Boko Haram sun sace mutum 2 da kayan abinci a Borno

Wata majiya ta ce sun shiga gida-gida suna harbi suna neman kayan abinci.

’Yan Ta’addan Boko Haram sun kai hari ƙauyen Kaleri da ke Ƙaramar Hukumar Jere a Jihar Borno, inda suka sace mutum biyu da kayan abinci masu tarin yawa.

Wata majiya daga yankin ta tabbatar da cewa lamarin ya faru ne kusa d Jami’ar Maiduguri (UNIMAID).

Majiyar ta ce, “Sun shigo da manyan makamai, suna harbe-harbe suna bi gida-gida don neman kayan abinci, suna sanya tsoro a zukatan mazauna garin.”

Wani mazaunin yankin da ya nemi a sakaya sunansa ya ce, “Sun yi garkuwa da mutane biyu, sannan suka kwashe kayan abinci.”

Bayan faruwar lamarin, jami’an ’yan sanda sun rufe yankin tare da kama wasu mutane, amma ba su bayyana cewar waɗanda suka kama na da alaƙa da harin ba.