Rundunar ’Yan Sandan Jihar Borno, ta kama wasu matasa uku da ake zargi da satar kekunan ɗinki guda 19 a cibiyar koyon sana’a ta Dala Lawanti da ke Maiduguri.
A cewar ’yan sanda, wani mai gadi a cibiyar, Kaka Modu Mustapha, mai shekaru 34, ya haɗa baki da wasu matasa biyu – Bukar Mustapha mai shekaru 16 da Ibrahim Mohammed mai shekaru 17 – domin aikata satar a ranar 22 ga wata Maris, 2025.
- ECOWAS ta gyara cibiyar magance shan miyagun ƙwayoyi a AKTH
- Tinubu zai sake zama shugaban ƙasa a 2027 — Akpabio
Kakakin rundunar, SP Nahum Kenneth Daso, ya ce jami’an ’yan sanda daga yankin Bulumkutu, sun samu rahoto game da satar, inda suka gudanar da bincike tare da kama waɗanda ake zargin, ciki har da mai gadin cibiyar.
Ya ce an samu nasarar ƙwato kekunan ɗinki guda shida daga cikin 19 da suka sace, yayin da ake ci gaba da bincike domin gano sauran guda 13.
SP Daso, ya buƙaci al’ummar jiharda su kasance masu kula tare da kai rahoton duk wani abun zargi ga jami’an tsaro domin daƙile aikata laifuka.