Hukumar Kula da Zirga-Zirgar Ababen Hawa ta Jihar Kano (KAROTA) ta tabbatar da kama wasu manyan motoci guda biyu da ke makare da katan din giya sama da 2,000 wacce kudinta ya haura Naira miliyan 50.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun kakakin hukumar, Nabilusi Abubakar Kofar Na’isa.
- Yada bayanan ’yan ta’adda: Gwamnati za ta kafa wa BBC da Trust TV takunkumi
- Ranar ’yacin kai Ukraine: Mun rasa kashi 20 na iyakokinmu —Zelensky
A cikin sanarwar, Kofar Naisa, ya ce shugaban hukumar, Baffa Babba Dan’Agundi ya bai wa jami’in da ya kama motocin kyautar Naira miliyan daya, saboda yadda ya ki karbar cin hancin Naira 500,000 don sakin motocin.
A cewarsa, gwamnatin jihar ta haramta shigo da barasa da kuma kowanne nau’i na kayan maye a fadin jihar.
Dan’Agundi ya yaba wa jami’in wajen nuna kishi tare da jan hankalin sauran jama’a da su yi koyi da shi.
Halilu Kawo Jalo, jami’in da ya kama motocin, ya ce an damke manyan motocin ne ta hanyar amfani da masu ba da bayanan sirri.
“Mun tare motocin a kan hanyar titin Obasanjo zuwa yankin Sabon Gari da ke jihar.
“Sun ba ni cin hanci amma na ki karba saboda na san illar kayan shaye-shaye sannan haramun ne.
“Kuma na san koyarwar addinin Musulunci kan illar karbar cin hanci, wanda haka ne ya sa na yi abin da ya dace,” a cewarsa.
Baffa ya kuma yi kira ga jama’a da su rika bai wa hukumar goyon baya domin tabbatar da tsaro a fadin jihar.