’Yan sandan sun kama wani mutum na buhuna 300 na tabar wiwi a Fatakwal, babban birnin Jihar Ribas.
Kakakin rundunar ’yan sandan jahar, Nwonyi Emeka, ya ce jami’an da ke sintiri karkashin sashen leqen asiri na sashen C4i ne suka kama motar da aka makare ta da kayan mayen.
- Ana zargin mai unguwa da fyade da sa wa yarinya cutar HIV a Jigawa
- Sojoji sun kama masu kera haramtattun makamai a Filato
Ya ce an yi nasarar kamen ne bayan wata majiya ta tsegunta wa jami’an tsaro da ke sintirin, inda ba tare da bata lokaci ba, suka bi sawun motarf.
Nwobi Emeka ya ci gaba da cewa “Koda direban motar ya fahimci jami’anmu shi suke bi, sai ya nemi ya fita daga motar ya tsere, amma suka yi wa motar zobe suka kama shi
“A binciken da suka gudanar ne suka ga buhuna 300 da ake zargi suna dauke da tabar wiwi, wanda da zarar an gama binciken su kotu za a mika shi.”