✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sojoji sun kama masu kera haramtattun makamai a Filato

An kama makamai iri-iri da kuma masu kera su da yin safarar su a haramtacciyar masan'antar

Sojoji sun bankado wata masana’antar kera makamai ta bayan fage a yankin Vom da ke Karamar Hukumar Jos ta Kudu a Jihar Filato.

“An kuma kama wasu mutum biyu da ke hada bindigogin suke kuma safararsu ,” in ji kakakin rundunar soji ta Operation Safe, Kyaftin Oya James.

Ya bayyana cewa a yayin samamen, sojojin sun kama bindigogi 6 kirar AK-47, SMG 4 da  kuma pistol a haramtacciyar masana’antar makaman.

Sauran haramtattun makaman sun ha hada da bodin bindigogi kirar AK; kayan badin bindigogi, kwanson albarusai, jigidan harsasai da kuma kayan kiran bindigogi.

Kyaftin Oya James ya ce sojoji za su ci gaba da aiki tare da sauran hukumomin tsaro domin kamawa da kuma tabbatar da ganin masu aikata miyagun laifuka sun fuskanci hukunci.