✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Masarautar Adamawa ta tube Hakimin Ribadu

Majalisar Masarautar Adamawa ta tube rawanin Hakimin Ribadu da ke Karamar Hukumar Fufore da ke jihar, Alhaji Gidado Abubakar

Majalisar Masarautar Adamawa ta tube rawanin Hakimin Ribadu da ke Karamar Hukumar Fufore da ke jihar, Alhaji Gidado Abubakar.

Mukaddashin Sakataren masarautar, Alhaji Kabiru Bakari, na ya sanar da hakan a cikin wata takarda da ya aike wa tubabben hakimin.

“Majalisar Masarautar Adamawa ta umarce ni da in rubuta in kuma sanar da kai cewa Gwamnan Jihar Adamawa ya amince da korar ka.

“Ka mika duk wasu takardun hukuma da ke hannunka, ciki har da takardar shaida, ga Mukaddashin Sakataren Masarautar Adamawa da ke Yola,’’ in ji wasikar.