✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sarakunan Arewa mazauna Kudu sun yi watsi da batun dakatar da Sarkin Sasa

Mun amince Ali Dahiru Zungeru ne Sarkin Hausawan kasar Ibadan, babu wanda yake jayayya da wannan matsayi.

Wasu Sarakunan Hausawa da Fulani da shugabannin ‘yan Arewa a Jihohi 17 na Kudancin Najeriya, sun mayar da martani a kan batun dakatar da Shugaban Majalisar ta su, Sarkin Sasa kuma Sardaunan Yamma, Alhaji Haruna Maiyasin, wanda Majalisar Sarkin Hausawan Ibadan, Alhaji Ali Dahiru Zungeru ta ce ta yi.

Shugabannin dai sun yi tattaki daga garuruwansu na Kudancin Najeriya, inda a wannan Asabar suka isa Ibadan, babban birnin Jihar Oyo domin halartar taro da ‘yan jarida wanda aka yi a Fadar Sarkin Sasa.

Uban Garin Sasa, Alhaji Isa Nalado da Sarkin Samarin Shuwa-Arab na Jihohin Kudu da Sakataren Fadar Sarkin Sasa, Alhaji Adam Haruna Yaro su ne suka yi wa ‘yan jarida jawabi a madadin Majalisar Sarakunan.

Aminiya wadda ta halarci taron, ta ce Shugaban Majalisar Sarakunan Hausawa a Jihohi 17 na Kudu, Sarkin Sasa Alhaji Haruna Maiyasin bai halarci taron ba.

Sai dai wakilinmu ya tattaro bayanan da aka fara da raba wa ‘yan jarida kwafin takardar Satifiket mai dauke da kwanan wata 8 ga watan Yuni na shekarar 1983 da Fadar Mai Martaba Olubadan na Ibadan marigayi Oba Yesufu Oloyede Asanike ta mika wa Alhaji Haruna Maiyasin domin tabbatar da nada shi a kan Sarautar Sarkin Sasa.

Sai kwafin satifiket na biyu da ya fito daga Fadar Shugaban Kasa ta Abuja da ke dauke da kwanan wata 3/12/1994 da sa hannun Laftanar Y. Lawal, hadimin Shugaban Shugaban Kasa na wancan lokaci Janar Sani Abacha da yake tabbatar da nadin Sarkin Sasa a matsayin Sardaunan Yamma kuma Shugaban Majalisar Sarakunan ‘yan Arewa a Jihohi 17 na Kudancin Kasa.

Shi kuwa kwafin takarda ta uku yana kunshe ne da sa hannun Sarakunan ‘yan Arewa 44 da suka nuna amincewarsu da wadannan mukamai da Fadar Olubadan da Ofishin Shugaban Kasa suka ba Sarkin Sasa.

A bisa wannan dalilai ne Shugabannin suka shaida wa ‘yan jarida cewa ba su ga dalilin da Sarkin Hausawan Ibadan yake jayayya da wannan matsayi da Allah ya daukaka Sarkin Sasa da shi ba.

Sun ce Sarkin Sasa mutum ne mai biyayya ga Fadar Olubadan na Ibadan, sabanin yadda masu adawa suke cewa ya ki yin biyayya ga wannan Fada Mai Alfarma.

A cewarsu, “Mun amince Alhaji Ali Dahiru Zungeru ne Sarkin Hausawan kasar Ibadan, babu wanda yake jayayya da wannan matsayi.

“Saboda haka bai kamata wasu mutane su kirkiro hanyar da za ta iya tayar da zaune tsaye a tsakanin al’ummar Arewacin Kasa da ke zaune a wannan yanki ba.”

Masu magana a madadin Majalisar, sun yi kira ga Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar da Sarakuna da Gwamnonin da ‘yan Majalisun Tarayya da na Jihohin Arewa su yi watsi da bayanan dakatar da Sarkin Sasa da ake watsawa a kafofin labarai domin a cewarsu bayanai ne da za su iya tunzura jama’a.

Sun bayyana cewa, “yau shekaru 40 da suka wuce kenan da Sarkin Sasa ya sadaukar da kansa da dukiyarsa babu dare babu rana yana daukar matakan shiga tsakani a kan rikice-rikicen manoma da makiyaya da ke zaune a wannan sashe.

“Babu wanda bai san da wannan mataki da wannan tsoho yake dauka wajen kare hakkin ‘yan Arewa mazauna wannan sashe ba.”

Haka kuma taron ya nemi Gwamnonin Jihohin Kudu su yi watsi da irin wannan bayanan tayar da husuma musamman a jihohinsu.