✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An kama mai abincin sayarwa da ke girki da ruwan wanke gawa

Ta ce duk wanda ya ci abincinta sai ya sake dawo kuma tana samun ciniki sosai.

’Yan sanda a Jihar Akwa Ibom sun cafke wata mai abincin siyarwar da ake zargin ta da amfani da ruwan wanke gawa.

Asirin mai abincin da ke layin Itam a Garin Uyo ya tonu ne bayan ma’aikacin dakin ajiyar gawan da take sayen ruwan wankan gawar ya ce ta ki biyan shi bashin kudin ruwan da ta saya tsawon wata uku.

Muutmin ya ci gaba da cewa kullum sai ta je wurinsa sau biyu zuwa uku tana sayen ruwan wanke gawar, inji majiyarmu.

’Yan sanda masu bincike sun ce matar ta tabbatar musu da cewa tana amfani da ruwan da aka wanke gawa a abincin da take sayarwa.

Ta ce tana yin haka ne saboda idan mutum ya ci abincinta to duk inda ya ci abinci ba zai gamsu ba sai ya dawo wurinta kuma tana samun kudi sosai.

Zuwa yanzu dai an kai matar Hedikwatar ’Yan Sanda da ke gari Uyo babban birnin jihar ana ci gaba da binciken ta.